Sarkin Musulmi ya maganta akan hare-haren Fulani

Sarkin Musulmi ya maganta akan hare-haren Fulani

- Sarkin Musulmi yayi Allah wadai da hare-haren da Fulani suke kaiwa a fadin Najeriya

- Sarkin Musulmi ya nuna rfashin jin dadin shi akan yadda har yanzu ba'a kama masu laifin ba

- Sarkin yayi kira ga yan Najeriya da kada su alakanta hare-haren da Addini ko wata kabila

 

Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar na 3, Sarki mafi daraja a Tarayyar Najeriya, ya maganta akan hare-hare da makiyaya suke kaiwa a fadin Tarayyar Najeriya.

Sarki Sa'ad kuma wanda shine shugaban kungiyar Jam'atul Nasril islam, ya gargadi mjtane akan alakanta hare-haren akan wani addini ko kuma wata Kabila.

Sarkin ya nemi da a hukunta duka wadanda aka kama da laifi da doka domin a tabbata cewa an kawo karshen tashin hankalin.

Sarkin Musulmi ya maganta akan hare-haren Fulani
Wani makiyayi da Bindiga kirar AK-47

Sarkin yace " Kungiyar Jam'atul Nasril Islam, ta samu labarin hare-hare da kuma barna akan dukiyoyin mutane dana gwamnati musamman a Agatu, Jihar Benue, Uzo-Uwanni a Jihar Enugu, da wasu sassa a jihar Nasaraw.

" A cikin kwanki kalilan munji an kai hare-hare a wurare da yawa kuma ba'a kama ko suwa nene ba.

" Muna kira da ayi bincike sosai, sannan kuma a hukunta ko suwa nene keda laifi.

" Abun takaici ne yadda wasu mutane suke kokarin alakanta abun da addini ko kuma wata kabila, kamataye mu dage wajen ganin wanzuwar zaman lafiya.

Idan zaku iya tunawa, sojojin Najeriya sun sha alwashin  yin duk wani abu da zasu iya domin ganin cewa sun kawo karshen hare-hare da ake kaiwa a Arewa ta tsakiya da kuma wasu sassan kasan nan.

Sun bayyana cewa duk wanda aka kama za'a yi mashi hukunci kamar dan tra'addan Boko Haram. Sun kuma yi kira da makiyayan su daina kai harin.

A wani labarin kuma, makiyaya a fadin Najeriya sun bayyana cewa babu wanda ya isa ya hana su yawo nema ma dabbobin su abinci. Sun bayyana cewa kundun tsarin mulkin Najeriya ya ba kowa dama daya zagaya inda yake so a fadin Najeriya. Sun kuma yi watsi da wa'adin da wata kungiya a kudu maso gabashin Najeriya ta basu akan su tashi daga yankin.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kawo karshen hare-haren, inda ya nemi yan Najeriya su zauna lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng