Dalilai 5 da suka sa na kulla harkar kasuwancina da PayWithSpecta

Dalilai 5 da suka sa na kulla harkar kasuwancina da PayWithSpecta

A matsayina na dan kasuwa, na kasance ina ta fadi-tashin samun kamfanin da zai tamakamin wajen biya wa abokanan huldata bukatunsu da kuma samar da farashi mai dorewa.

Saboda da canjawar yanayin kasuwanci a Najeriya, hukumomi da masu ma’amala suna tsintar kansu cikin mawuyacin hali wajen gudanar da kasuwancinsu ta hanyar samun mamora.

Hadarin da ke cikin harkokin kasuwanci a yanzu ya yawaita matuka, ta hanyar yadda ake canza dokoki, inda za ka tarar kafin kiftawar ido, kasuwanci ya durkushe.

Na shafe shekaru masu yawa ina kokarin lalubo hanyar da zan magance wadannan matsaloli, haka kuma zan ci gaba da kokarin zakulo hanyoyin da za su taimaka wajen samar wa abokanan huldata mafita.

Daya daga cikin mafitar da na samu ita ce manhajar kamfanin PayWithSpecta.

PayWithSpecta manhaja ce wacce za ta taimaka wajen yi wa abokanan huldarmu rajista da za su iya biyan kudin kayan da suka saya, wanda za a biya kudin kayan da aka saya gaba daya.

Yanayin da za a kira wannan tsarin da shi, sai dai a ce ribar kafa! Wannan mafita da na samu tana da mutukar ban-kaye ga harakar kasuwanci.

Saboda na samu wani abu na musamman da zan samar wa abokanan huldata, akwai dalilan da suka sa na zabi PayWithSpecta domin huldar kasuwnaci a Najeriya.

Dalilai 5 da suka sa na kulla harkar kasuwancina da PayWithSpecta
Dalilai 5 da suka sa na kulla harkar kasuwancina da PayWithSpecta
Source: UGC

Shuhura

Manhajar PayWithSpecta ta karade wurare masu yawa. Akwai ’yan Najeriya sama da dubu 100,000 da suka yi rijista da MySpecta; wanda yake samar da bashi a cikin minti 5.

Dalilin rijistar da na yi da su, ya sa na samu kwararowar abokanan hulda.

Don haka yin rijista da PayWithSpecta dama ce wajen tallata haja kamar yadda kasuwancina yake habaka a yanzu wanda na samu daruruwan abokanan hulda wadanda tuni suka yi rijista da PayWithSpecta.

Samun jarin da za a fara hulda da shi a yanzu shi ne babban kalubale da yake kawo wa ’yan Najeriya tsaiko a yau, sakamakon yadda mutane ke neman kudi a hanu domin gudanar da kasuwancin da zai taimaki rayuwarsu.

Na tabbatar da cewa PayWithSpecta shi ne babban jigo wajen taimakon ’yan Najeriya su samu kudin da za su gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Samun moriya

A matsayina na dan kasuwa burina shi ne, na samu ci gaba; ina so yau ta fi jiya kyau, sannan kasuwancina ya habaka ta hanyar cinikayya.

Tsadar rayuwa a ’yan shekarun nan, ta hanyar karyewar farashin Naira da kuma sauran tasgaro da aka samu, ya jefa abokanan huldata cikin mawuyacin hali wanda ba sa iya sayan abubuwan da suka saba saya a baya.

Saboda haka na fara lalubo hanyar da zan habaka cinikina ta hanyar samar wa abokanan huldata damar da za su ci gaba da sayan kaya a wajena.

Babu gaggawar neman abokan hulda

A wasu lokutan, Ina da abokanan huldan da suke son sayan kaya a gareni amma ba su da kudi a hanu da za su biya kudin kaya.

Sakamakon kwarewa da nake da ita wajen kasuwanci ina bi sannu a hanakli wajen bayar da bashin kaya ga abokan huldata saboda gudun abin da ka je ya zo, hakan kuma yana kawo min tsaiko wajen ciniki.

Amma a yanzu abokan huldata za su iya sayan kaya bashi, sannan su biya daga baya ni kuma alhali na karbi kudina a dunkule.

Wannan al’amari yana da bankaye sannan kuma akwai riba daga kowane bangare.

Bani da damuwa a kayan da na sayar bashi ga abokan huldata, sannan shi kansa abokin hulda ba shi da damuwa.

Kamfanin PaywithSpecta shi ne zai dauki wannan kasada ta inda za ka samu kudin kayanka a jumlace sannan kowa yana cikin farin ciki.

A duk inda shagonka yake kana iya amfani da PaywithSpecta

Za a iya amfani da PayWithSpecta ta hanyar shagon intanet ko shago na zahiri ko duka biyun.

Wannan ne ya sake fito da kyawun wannan hulda na kasuwanci. Ba sai abokanan hulda sun riki kudi a hanu ba, abin da zai yi kawai shi ne su bayar da lambarsa ta Specta ID a lokacin da suka gama sayayya, sai kai kuma ka yi amfani da manhajar PayWithSpecta domin ka tabbatar ka samu kudinka nan ta ke.

Karbi bashi don ka tallafi kasuwancinka

Kamfanin PayWithSpecta yana bayar da wannan dama; kai dai yi rijista don cin gajiyar wannan dama.

Wannan hanya ta taimaka min wajen fadada kasuwancina, sannan na samu damar gudanar da huldodina ta hanyar amfani da damar da PayWithSpecta ta bayar.

Me kake jira? Ka yi rijsta ta nan: www.paywithspecta.com/merchant

Source: Legit.ng

Online view pixel