Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun

Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun

- Wata tanka dauke da akalla litoci 50,000 na man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun, Oke-Mosan

- Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar

- Rahotanni sun bayyana cewa sai da jami'an hukumar kashe gobara suka kawo agaji kafin aka samu damar kashe wutar

Wata tanka dauke da akalla litoci 50,000 na man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun, Oke-Mosan, Abeokuta.

Wakilin jaridar The Punch ya ruwaito cewa tankar ta fito ne daga Ijora, jihar Lagos, a hanyarta ta zuwa Adatan, a cikin garin Abeokuta.

Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: Kotu ta hana EFCC takardar izinin cafke Diezani Alison-Madueke

Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun
Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun - Sahara Reporters
Asali: UGC

Matukin tankar, wanda ya bayyana kansa da suna Nurudeen Yusuf, ya shaidawa manema labarai cewa, yana tare da yaran motarsa guda biyu, suka ga wutar ta kama daga injin motar.

Shugaban hukumar kashe gobara na gwamnatin tarayya reshen jihar, Sodiq Atanda, ya ce, sai da jami'an hukumar suka kawo agaji kafin aka samu damar kashe wutar.

KARANTA WANNAN: Zaben 2023, Muna rokon a ba Kudu maso Gabas shugabancin kasa - Gwamna Umahi

Atanda ya ce, "Ba don Allah ya sa ofishinmu na kusa ba, kuma jami'anmu na jiran ko ta kwana, da wannan gobarar ta munana sosai."

Sai dai, ya bayyana cewa, tankar man ba ta dauke da tukunyar kashe gobara.

A wani labarin, Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa muhimman wurare 22 mabarnata suka lalata a ta'adin da batagari ke cigaba da yi a sassan Nigeria.

Batagarin matasa sun fake da zanga-zangar ENDSARS wajen fara balle wuraren ajiyar kayayyaki mallakar gwamnati da daidaikun mutane.

Haka zalika, sun kuma shiga gidajen manyan 'yan siyasa tare da yin awon gaba da duk kayayyakin da ke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel