Da duminsa: An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke Jos

Da duminsa: An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke Jos

- An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke jihar Jos, inda aka kai su asibitin koyarwa na jihar

- Ana zargin gawawwakin mutanen da suke tsoron jami'an tsaro su damkesu a kan satar da aka yi a gidan Dogara ne

- Dama a ranar Asabar da ta gabata ne bata-gari suka yi sata a gidan tsohon Kakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara

An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke jihar Filato, Jos, jaridar Newswire ta wallafa.

Jaridar Daily Trust ta bayyana hakan, inda tace gawawwakin mazauna wurin ne wadanda suka fada cikin tafkin ne don gudun kada jami'an tsaro su kama su a makon da ya gabata a matsayin wadanda suka yi sata a gidan tsohon sanata, Yakubu Dogara, a Jos.

A ranar Lahadi da safe ne wasu bata-gari suka balle gidan tsohon Kakakin majalisar dattawan, inda suka kwashe tsadaddun abubuwa daga gidan.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka sanya wa mazauna Jos kullen awanni 24 a jihar, bayan sun balle ma'adanar gwamnati da ke Dogon Dutse a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar.

Bayan saka kullen ne aka yi ta sace-sace a ma'adanan gwamnatin Jos da Bukuru, inda suka kwashi kayan abinci.

Omini Bridget, jami'ar hulda da jama'a ta asibitin koyarwa da ke Jos, ta tabbatar da tsintar gawawwakin guda 4 a tafkin bayan kawo su asibitin.

Amma wata majiya daga wuraren Laminga ta ce gawawwakin da aka tsinta guda 8 ne, an kai wasu gawawwakin wasu asibitocin ne daban.

KU KARANTA: Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

Da duminsa: An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke Jos
Da duminsa: An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke Jos. Hoto daga @newswirengr.com
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London

A wani labari na daban, sojojin da ke tsaron asibitin sojoji na Ikoyi a jihar Legas sun dakatar da masu bincike a kan kisan masu zanga-zangar EndSARS daga shiga ma'adanar gawawwakin asibitin.

Masu binciken sun isa asibitin a ranar Juma'a ba tare da sanar da zuwan nasu ba, don su yi bincike a kan kashe-kashen da ake zargin sojoji sun yi a Lekki Toll gate.

Wadanda al'amarin ya faru a gabansu, sun zargi sojoji da kwashe gawawwakin take a nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng