Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya

Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya

- Gwamnatin jihar Kano za ta fara kama masu magagungunan gargajiya da ke amfani da kalaman batsa don tallata hajojinsu

- Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya sanarwa manema labarai a ranar Laraba, inda yace yanzu haka an samar da wani kwamiti

- Ya ce kwamitin zai hada da ma'aikatar lafiya, jami'an KAROTA da na Hisbah za su dinga kama masu magungunan gargajiyar

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fara kama masu magaungunan gargajiya da suke amfani da kalamen batsa wurin tallar magungunansu, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kirkiri wani kwamiti da ke karkashin kwamishinan lafiya, Dr Ibrahim Tsanyawa, KAROTA, Hisbah da sauran jami'an tsaro a matsayin 'yan kwamitin.

Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba, inda yace an gama duk wasu shirye-shirye don fara ayyuka a kwamitin.

Ya ce jami'an Hisbah da na KAROTA ne za su dinga kama masu magungunan gargajiyar su gabatar da su kotu.

Ya kara da cewa, suna tsananta amfani da kalaman batsa wurin tallata hajojinsu wanda gwamnati ba za ta lamunci hakan ba.

KU KARANTA: Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da tsakiya - Buhari

Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya
Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

A wani labari na daban, wani rikici ya na ta ruruwa a masarautar Alade Idanre da ke jihar Ondo a kan wanda zai gaji Olusegun Akinbola, sarkin masarautar da ya rasu a ranar 16 ga watan OKtoba.

Bayan kwana biyu da rasuwar sarkin, an nada Temilowa Akinbola, diyarsa ta farko a matsayin sarauniyar rikon kwarya. Bayan kwanaki 5 da nada ta, wasu 'yan ta'adda suka shigo fadar suka kai mata farmaki tare da mahaifiyarta, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel