Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara

Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara

- Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli, ya kai ziyara ta musamman ga sarkin Kano, Aminu Bayero

- Ya kai ziyarar ne don kara dankon dadadden zumuncin da ke tsakanin masarautun biyu

- Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya taya Bamalli murnar nasarar zama sarkin Zazzau na 19

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli ya kai wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero ziyara ta musamman jiya, don kara dankon zumuntar da ke tsakanin masarautun guda biyu.

Ya ce ya kai ziyarar ne don kara dankon zumuncin da ya dade tsakanin masarautar Zazzau da ta Kano tun lokacin Sheikh Usman Fodio, Daily Trust ta wallafa.

Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara
Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara. Hoto daga @HrhBayero
Asali: Twitter

Sarkin ya lura da yadda masarautun guda biyu suka dade cikin kaunar juna tamkar 'yan uwa, kuma yana fatan soyayyar ta tabbata.

KU KARANTA: Zakara ya kashe jami'in dan sanda har lahira da wuka

A cewarsa, "Muna sane da zumuncin da ya dade tsakanin marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara
Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara. Hoto daga @HrhBayero
Asali: Twitter

"Duk abinda ya shafi Kano, to hakika ya shafe mu, ba wai don makwabtaka ba, sai don mun riga mun zama 'yan uwan juna."

"Inaso in sanar da ku cewa duk gidajen sarautar Zazzau 'yan uwa ne. A wannan mulkin, akwai wakilai daga kowanne gida.

Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara
Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara. Hoto daga @HrhBayero
Asali: Twitter

"Kashi 95 cikin 100 na masu sarautar Zazzau da shugabannin anguwanni na iyakar kokarin kawo cigaba a masarautar," cewar Bamalli.

Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara
Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara. Hoto daga @HrhBayero
Asali: Twitter

Sanannen Sarki Bayero ya taya Bamalli murnar samun nasarar zama sarkin Zazzau na 19, kuma ya bayyana hakan a matsayin nasara.

KU KARANTA: Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

A wani labari na daban, wani rikici ya na ta ruruwa a masarautar Alade Idanre da ke jihar Ondo a kan wanda zai gaji Olusegun Akinbola, sarkin masarautar da ya rasu a ranar 16 ga watan OKtoba.

Bayan kwana biyu da rasuwar sarkin, an nada Temilowa Akinbola, diyarsa ta farko a matsayin sarauniyar rikon kwarya. Bayan kwanaki 5 da nada ta, wasu 'yan ta'adda suka shigo fadar suka kai mata farmaki tare da mahaifiyarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel