Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa

Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa

- Mummunan rikici ya barke a masarautar Alade Idanre da ke jihar Ondo a kan wanda zai gaji sarautar

- Bayan rasuwar sarki Olusegun Akinbola ranar 16 ga watan Oktoba ne aka nada diyarsa ta fari don rikon kwarya

- Kwanaki 5 da nadin ne wani Basarake ya tura 'yan ta'adda suka shiga fadar da bindigogi da makamai suka rikita ko ina

Wani rikici ya na ta ruruwa a masarautar Alade Idanre da ke jihar Ondo a kan wanda zai gaji Olusegun Akinbola, sarkin masarautar da ya rasu a ranar 16 ga watan OKtoba.

Bayan kwana biyu da rasuwar sarkin, an nada Temilowa Akinbola, diyarsa ta farko a matsayin sarauniyar rikon kwarya.

Bayan kwanaki 5 da nada ta, wasu 'yan ta'adda suka shigo fadar suka kai mata farmaki tare da mahaifiyarta, The Cable ta wallafa.

A wata takarda da ta gabatar wa da kwamishinan jihar, ta bayyana yadda Frederick Arolaye, babban basaraken Idanre, ya turo 'yan ta'adda suka ci zarafinta a cikin fadar mahaifinta.

KU KARANTA: Sanwo-Olu ya fusata da rikicin kabilanci, ya yi tsokaci mai zafi

Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa
Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

Kamar yadda lauyanta ya rubuta a wata takarda da sarauniyar ta sa hannu, "Wacce mu ke karewa ta sanar da mu cewa a ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba 2020, wasu 'yan ta'adda kusan 20, sun shigo fadar sarkin Alade da karfi da yaji, inda suka tayar da hankulan mutane.

"Bata-garin sun zo a babura ne, suna dauke da bindigogi, adduna, itace da sauran munanan makamai.

"A yadda ta bayyana mana, sun harbi iska, suna wakar yaki sannan suka bukaci a bayyanar da sarauniya mai rikon kwaryar."

"Yan ta'addan sun lalata duk wasu ababen hawa da aka ajiye a harabar fadar. Sun kuma farfasa duk wasu tagogi masu gilashi, da na motocin basarakiyar, bakinta da fadawanta."

"Bayan shigarsu cikin dakunan fadar, sun kwashe wayoyin salula, kayan abinci, sutturu, kudade, kwamfiyutoci, sarkoki da sauran kayan alatu da ke masarautar."

A wani labari na daban, a taron da FEC tayi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya amince da biyan Naira Biliyan 4.5 don samar da takardun jarabawa da kuma gyaran titinan da ke kauyakun babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanarwa manema labaran cikin gidan gwamnati, tare da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad, inda yace an ware Naira biliyan 2.9 don samar da kayan jarabawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel