Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da tsakiya - Buhari

Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da tsakiya - Buhari

- Ina matukar farin cikin yadda mulkina ya samar da tsaro da kwanciyar hankali a arewacin Najeriya, cewar Buhari

- A cewarsa,mulkinsa ya samar da tsaro a arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya wanda ba'a samu ba tun 1960

- Ya fadi hakan ne a wata takarda da mai bashi shawara na musamman a harkar yada labarai, Femi Adesina, yasa hannu a ranar Laraba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa ya kawo karshen rashin tsaro a arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya.

A wata takarda da mai bashi shawara na musamman a kan harkar yada labarai, Femi Adesina ya saki a ranar Laraba, ya bayyana inda shugaba Buhari ya fadi hakan lokacin da ya ke kaddamar da ranar tunawa da sojoji ta 2021.

Kamar yadda shugaban kasa yace, ana yin wannan taron ne don tunatar da 'yan Najeriya yadda za su yi kishin kasa da kuma kawo hadin kai tsakanin 'yan Najeriya, wanda yayi wahala matuka kafin ya kai wannan matakin.

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma - Buhari
Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma - Buhari. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar

Buhari ya roki 'yan Najeriya da su kiyaye yin abubuwan da za su kawo rabuwar kawuna tsakaninsu.

Shugaban kasa ya kara da cewa, jami'an tsaro sun yi iyakar kokarinsu wurin kawo zaman lafiya arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya. Don yanzu haka arewa na cikin kwanciyar hankali.

A cewarsa, "kasarmu ta fuskanci kalubale iri-iri a harkar tsaro tun da Najeriya ta samu 'yancin kanta.

"Wadannan kalubalen ya jawo tattalin arzikin Najeriya, ilimi, harkokin lafiya da na noma sun yi kasa.

"Ina farin cikin yadda aka samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas da tsakiyan arewacin Najeriya."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don sake yin shekaru 5 a kan kujerar.

Bayan wa'adin mulkinsa na haramar karewa, shugaban kasar ya sake nada shi. Wasu suna kawo sunayen mutane da dama da suke tunanin shugaban kasa zai nada, ashe ba ta nan gizo ke saka ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel