Zaben 2023: Muna rokon a ba Kudu maso Gabas shugabancin kasa - Gwamna Umahi

Zaben 2023: Muna rokon a ba Kudu maso Gabas shugabancin kasa - Gwamna Umahi

- Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi yayi magana akan zabar sabon shugaban kasa daga bangaren sa a shekarar 2023

- Yace matasan yankin kudu maso gabas sun bayyana musu kudirinsu na samun shugaban kasa daga yankinsu, wanda yace zai sanar da Buhari

- Sunyi wannan tattaunawar ne da shugabannin matasa a ranar Talata akan yadda za'a kawo karshen zanga-zangar EndSARS, anan ne suka gabatar da kudirinsu

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi, yace babban burin matasan kudu maso gabas bai wuce shugaban kasan Najeriya yazo daga bangarensu ba a 2023.

Umahi ya fadi hakan a ranar Talata a wani taro da akayi a Abakaliki, yace shugabannin kudu maso gabas sunyi wani taro da shugabannin matasa, inda suka amince da ajiye makamansu akan zanga-zangar EndSARS don samar da zaman lafiya.

KARANTA WANNAN: Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

Zaben 2023: Gwamna Umahi ya bukaci a kai tikitin shugaban kasa shiyyar Kudu maso Gabas
Zaben 2023: Gwamna Umahi ya bukaci a kai tikitin shugaban kasa shiyyar Kudu maso Gabas - Punch Newspapers
Asali: UGC

A cewar Umahi, "Ina tunanin idan lokacin zaben sabon shugaban kasa yayi, a ba wa dan Kudu maso gabas damar mulki, don na tabbatar burin matasan kenan.

Ya kara da cewa, "Mun tattauna sosai da matasan, sun bukaci mu tattauna da shugaban kasa akan kudirinsu.

"Sunce zasu daina duk wata zanga-zangar matsawar aka samar musu da abinda sukeso. Kuma shugaban kasa ya fahimcesu, kuma yace zai duba ya gani.

KARANTA WANNAN: DPO ya labarta yadda wasu fusatattun matasa suka so halaka shi a Kubwa

"Munyi alawadai akan harbin da akayi a Lekki, kuma zamu tabbatar anyi bincike mai tsanani sannan duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma.

"Shugabannin mu nanan suna kokari akan lamarin da matasan kudu maso gabas suka taso dashi.

"Mun amince da saka matasa a cikin kasafin kowacce shekara. Sun bukaci a gyara titunan jihohinsu, wanda yanzu haka gwamnatin tarayya ta fara aiki akai."

A wani labarin, A ranar Litinin ne rundunar 'yan sanda ta cafke wasu miji da mata, Mr da Mrs Philip Iboko, bisa zarginsu da azabtar da wata yarinya mai shekaru takwas da haihuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano iyalan suna azabtar da yarinyar ne biyo bayan bullar wani bidiyo a yanar gizo da ke nuna yadda aka shanya yarinyar a rana bayan da aka daure kafafunta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel