'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami

'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami

- Bayan masu zanga-zangar EndSARS sun balle gidajen gyaran hali, inda 'yan gidajen suka tsere

- 'Yan sandan jihar Edo sun samu nasarar damkar 10 daga cikin wadanda suka tsere daga gidajen gyaran hali

- An kama wasu daga ciki suna fashi da makamai, daya kuma yana yunkurin kashe wanda yayi shaidarsa a kotu

'Yan sandan jihar Edo sun samu nasarar damkar 'yan gidan gyaran hali 10 da suka gudu daga gidan gyaran halin Benin Medium Custodial Centre da na Oko Medium Custodial Centre dake Benin, babban birnin jihar Edo.

An kama 6 daga cikinsu yayin da suke kokarin yin fashi da makami, daya kuma yana yunkurin kashe wanda yayi shaidar tabbatar da laifinsa a kotu, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan gidan gyaran halin 10 suna cikin mutane 126 da aka kama, inda ake zarginsu da fasa ma'adanar hukumar kwastam, Central medical Store's Warehouse, Olam Nigeria PLC Privacy Warehouse da Blessed Doris-Dey Warehouse da ke kan titin Benin-Agbor.

Yayin da aka tattarosu, kwamishinan 'yan sandan jihar, Johnson Kokumon, ya ce an kama 28 daga cikinsu ne da laifin sata a ma'adanar kwastam, 45 kuma na ma'adanar magunguna, 13 na Olam sai 16 na ma'adanar Dorisday.

Ya bayar da sunayen wadanda aka kara kamawa, inda yace akwai Emmanuel Udoh, Friday Etim, Victor Akpotor, Lucky Precious, Osarumen Enoragbon, Patrick Eguavoen, Abraham Matthew, Endurance Ifobuow, Mohammed Adamu da Henry Atadi.

KU KARANTA: Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5

'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami
'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya sabunta nadin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Cross River sun sanar da kama Johnson Richard-Inem a ranar Litinin, ana zarginsa da kirkirar dabarar satar dukiyoyin gwamnati da wulakanta su ranar 24 ga watan Oktoba a Calabar International Conference Centre.

Hukumar ta bayyana yadda aka amso fiye da kujerun alfarma 1000, shimfidu na alfarma da sauran tsadaddun abubuwa daga hannunsa, Premium time ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel