FEC ta amince da fitar da N4.5bn domin titunan FCT da buga takardun jarabawa

FEC ta amince da fitar da N4.5bn domin titunan FCT da buga takardun jarabawa

- A taron da FEC tayi, wanda shugaba Buhari ya jagoranta, ta amince bayan Naira biliyan 4.5, don samar da takardun jarabawa da gyaran tituna a Abuja

- Ministan ilimi, Adamu Adamu da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad suka sanar da hakan yayin da suke tattaunawa da manema labarai

- Kayan jarabawar sun hada da na azuzuwan karshe na firamare da na sakandare, da kuma titunan kauyakun da ke Abuja

A taron da FEC tayi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya amince da biyan Naira Biliyan 4.5 don samar da takardun jarabawa da kuma gyaran titinan da ke kauyakun babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanarwa manema labaran cikin gidan gwamnati, tare da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad, inda yace an ware Naira biliyan 2.9 don samar da kayan jarabawa.

KU KARANTA: Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3

FEC ta amince da fitar da N4.5bn domin titunan FCT da buga takardun jarabawa
FEC ta amince da fitar da N4.5bn domin titunan FCT da buga takardun jarabawa. Hoto daga @Dailytrust
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya sabunta nadin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Kayan jarabawar sun hada da na jarabawar azuzuwan karshe na firamare da na sakandare da na shiga sakandare.

"Sakamakon wannan rikicin ne yasa muka dage lokacin yin jarabawoyin," a cewar ministan.

Ministan babban birnin tarayya, Muhammed Bello, yayin da yake jawabi, ya ce FEC ta amince da biyan Naira 1,619,701,391.14 don gyaran wasu tituna dake cikin Abuja, Daily Trust ta wallafa.

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan. Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Sun cigaba da satar dukiyoyin gwamnati wadanda suka hada da kayan tallafin COVID-19, kayan shaguna, kasuwanni da sauran dukiyoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel