Zakara ya kashe jami'in dan sanda har lahira da wuka

Zakara ya kashe jami'in dan sanda har lahira da wuka

- Wani zakara ya kashe dan sanda da wata wuka da ke makale da kafarsa a kasar Philippine

- Philippines suna da wata al'ada ta makalawa zakaru 2 wukake a kafafunsu su yi dambe don nishadi

- Zakaran ya yanki dan sandan ne a cinya, wanda yayi sanadiyyar yanka wata jijiya a cinyarsa

Wani zakaran kokuwa yayi ajalin wani dan sandan Philippine da wukar dake makale a kafarsa, a cewar wasu jami'ai ranar Laraba, jaridar The Nation ta wallafa haka.

An hanzarta da Christian Bolok, shugaban 'yan sandan garin San Jose da ke arewacin Samar, asibiti bayan faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya mutu take-yanke.

Ya jagoranci 'yan sanda wurin dakatar da gasar damben zakaru a wani kauye da ke San Jose, inda ya dauki daya daga cikin zakarun.

Wata wukar karfe dake makale da kafar zakarar ta yanki cinyarsa, wacce ta kaiga datsa jijiyoyin cinyarsa, cewar Arnel Apud, babban jami'in 'yan sanda.

"Naji radadin rasa dan uwa da ya rasu a sanadin yin aiki ga al'umma," a cewarsa a wata takarda.

"Al'amarin bashi da dadin ji, sai dai kaddara ta riga fata."

An kama mutane 6 da ake zargin sun shirya kokuwar zakarun, cewar Apud.

Kokuwar zakaru wata al'adar Philippines ce, wacce ake yi yawanci a karshen mako. Za'a samu zakarun da aka horar a kan kokawar, a saka su a wani kebabben wuri, suna makale da wuka a kafafunsu, wacce za ta yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin zakarun.

KU KARANTA: Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5

Zakara ya kashe jami'in dan sanda har lahira da wuka
Zakara ya kashe jami'in dan sanda har lahira da wuka. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Cross River sun sanar da kama Johnson Richard-Inem a ranar Litinin, ana zarginsa da kirkirar dabarar satar dukiyoyin gwamnati da wulakanta su ranar 24 ga watan Oktoba a Calabar International Conference Centre.

Hukumar ta bayyana yadda aka amso fiye da kujerun alfarma 1000, shimfidu na alfarma da sauran tsadaddun abubuwa daga hannunsa, Premium time ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng