Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar

Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar

- Dama gwamnatin jihar Cross River ta umarci wadanda suka saci dukiyoyin gwamnati da su mayar da su cikin awanni 24

- Ashe kuwa suna da tsumi da dabarar amsowa, don a ranar Lahadi, 'yan sandan jihar suka bi gidaje da kayan gida don yin bincike

- Garin bincike sun gano wanda ya kirkiro yin satar mai suna Richard-Inem, an gano kujeru 1000, kilisai, AC da sauran kayan alatu a hannunsa

'Yan sandan jihar Cross River sun sanar da kama Johnson Richard-Inem a ranar Litinin, ana zarginsa da kirkirar dabarar satar dukiyoyin gwamnati da wulakanta su ranar 24 ga watan Oktoba a Calabar International Conference Centre.

Hukumar ta bayyana yadda aka amso fiye da kujerun alfarma 1000, shimfidu na alfarma da sauran tsadaddun abubuwa daga hannunsa, Premium time ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh, ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin cewa, an kama Richard-Inem wanda dama bakanike ne a Esuk Otu, kusa da NTA Calabar da wadannan kayayyakin.

KU KARANTA: Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar

Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar
Jerin kayayyakin da aka samu a gidan shugaban masu satar kaya a Calabar. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace matar basarake a jihar Kano

A cewar kwamishinan, "Mun kama wanda ake zargin sakamakon amfani da dabarar bin gidaje muna bincike a ranar Lahadi.

"Mun sanya kayan gida ne domin kada wani yayi zargin abinda muka zo yi kenan, shiyasa muka kama mutane da dama.

"Don haka duk wanda yasan bai mayar da kayan da ya dauka ba, mun bashi awanni 24 yayi gaggawar mayar da su. Yanzu haka mun samu nasarar amso kujeru na alfarma guda 1000, kilisai, AC da sauransu.

"Ba za mu cigaba da zama muna zura idanu ba; muna rokon shugabannin addini da na gargajiya da ke wurare daban-daban da su shawarci duk wadanda suka saci dukiyar da ba tasu ba su mayar."

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan. Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel