Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5

Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5

- Sojoji na cigaba da ragargazar 'yan Boko Haram a jihar Borno, duk da 'yan ta'addan na nemo sababbin dabarun kai wa sojojin hari

- A ranar Litinin ne gumurzu ya turnike tsakanin 'yan Boko Haram da sojoji da ke Damboa, bayan sun kai wa sojojin hari

- Sakamakon karon battan, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 22, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma sukaji raunuka

'Yan kungiyar Boko Haram 22 ne suka mutu, yayin da sojoji 5 suka rasa rayukansu sakamakon wani gumurzu daya turnike tsakanin Sojoji da 'yan ta'addan.

Wata majiya tace 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin da ke Damboa hari a ranar Litinin.

Sojojin sun ragargajesu na tsawon awanni 5. Sakamakon haka ne sojoji 5 suka rasa rayukansu, 2 kuma suka samu raunuka.

Yan ta'addan sun sace wata motar sojojin, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa

Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5
Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)

Wata majiya ta daban ta ce, "Gumurzu ya turnuke tsakanin sojojin Operation Lafiya Dole da 'yan Boko Haram, wanda sojoji suka yi kaca-kaca da su."

Duk da dai Kakakin rundunar, Sagir Musa, baya nan balle a ji ta bakinsa dangane da harin.

Dama sojoji 7 sun rasa rayukansu a ranar Alhamis. Rundunar na cigaba da kewaye wurin da 'yan ta'addan suka kai musu hari, bayan sun saka kayan sojoji.

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya yi wani taro da manyan shugabannin rundunar soji, duk wasu GOC da kwamandojin filin daga.

Kamar yadda The Nation suka tattaro bayanai akan taron da akayi a hedkwatar tsaro a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Buratai ya ce wa manyan jami'an soji su tabbatar sun zama masu juriya, don hargitsa Najeriya ba nasu bane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel