'Yan bindiga sun sace matar basarake a jihar Kano

'Yan bindiga sun sace matar basarake a jihar Kano

- Masarautar Karaye da ke jihar Kano ta sanar da satan matar sarkin kauyen Tsara da ke karamar hukumar Rogo

- A ranar Juma'a da misalin karfe 1 na dare 'yan bindiga suka fada gidan sarkin kauyen da bindigogi suka tafi da matarsa

- Har yanzu ba'a fahimci dalilinsu na yin hakan ba, don basu kira kowa sun sanar da kudin da suke bukata ba

Masarautar Karaye da ke jihar Kano ta sanar da satan matar sarkin kauyen Tsara da ke karamar hukumar Rogo, Aishatu Aliyu da wasu 'yan bindiga suka yi.

Kamar yadda sarkin Rogo (Wamban Karaye), Muhammadu Mahraz, ya kai wa Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II, rahoto, wasu 'yan bindiga sun shiga gidan sarkin kauyen Tsara, Aliyu Muhammad, da misalin karfe 1 na daren Juma'a, inda suka tafi da matarsa.

KU KARANTA: Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja

Kakakin masarautar, Haruna Gunduwawa, ya sanar da PREMIUM TIMES cewa ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka yi ta harbin iska kafin su dauki matar a gaban sarkin kauyen.

A cewarsa, sai da mazauna kauyen suka ga alburusai 17 washegarin faruwar lamarin.

Ya bayyana yadda da yawan 'yan kauyen suka kwana a daji a daren da lamarin ya faru don gudun mutuwa.

'Yan bindiga sun sace matar basarake a jihar Kano
'Yan bindiga sun sace matar basarake a jihar Kano. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya

Gunduwawa yace, har safiyar Talata, Masarautar ba ta fahimci dalilin satar matar ba, don har yanzu ba su kira kowa ba balle su sanar da kudin da za'a fanshe ta.

Kakakin Masarautar ya ce yanzu haka kusan mutane 4 kenan da aka yi garkuwa da su cikin watanni 2 a karamar hukumar Rogo, wacce iyaka ce tsakanin jihar Kano da Kaduna.

Yace sarkin karaye ya roki jami'an tsaro da su duba al'amarin kuma su dauki mataki a kai.

Ya kuma roki jama'a da su taya masarautar da addu'a don samun tsaro.

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan. Daily Trust ta ruwaito yadda bata-gari suka yi ta amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin satar dukiyoyin al'umma, duk da kullen da aka yi ta sakawa a jihohin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel