Da duminsa: Jirgin 'yan sanda ya tunkari sansanin 'yan bautar kasa da ke Abuja

Da duminsa: Jirgin 'yan sanda ya tunkari sansanin 'yan bautar kasa da ke Abuja

- Ana cigaba da samun sabbin rahotannin aikata barna kala-kala da wasu batagarin matasa ke yi a sassan Najeriya

- A ranar Talata ne wasu batagarin matasa suka afka sansanin masu bautar kasa da ke Abuja

- Shugaban hukumar kula da masu bautar kasa ya bayyana cewa babu kayan tallafin korona a sansaninsu

'Yan daba sun shiga sansanin 'yan bautar kasa da ke Kubwa a Abuja.

Babu wata-wata, da yawansu suka fara kwashe kayan abinci da katifun da aka zuba domin amfanin 'yan gudun hijirar sakamakon komawa da za su yi a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Jami'an tsaron da suka isa wurin sun donga harbin iska domin tsoratar da tsagerun amma babu wata biyan bukata.

Amma kwatsam, sai ga jirgin yakin jami'an 'yan sandan Najeriya ya tunkari wurin.

KU KARANTA: Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki

Wasu bata garin matasa a ranar Talata, 27 ga Oktoba, sun fasa sansanin masu bautan kasa ta NYSC dake unguwar Kubwa, birnin tarayya Abuja.

Da duminsa: Jirgin 'yan sanda ya tunkari sansanin 'yan bautar kasa da ke Abuja
Jirgin 'yan sanda
Asali: Twitter

Matasan sun wawashe katifu da wasu kayan alfanu.

KU KARANTA: Nigeria: Mabarnata sun haka fafakeken rami a titin da jirgin sama ke falfala gudu kafin ya tashi

Hakazalika, a garin Madalla a jihar Neja ya nuna cewa, wasu daruruwan matasa sun kai mamaya wani dakin ajiya mai zaman kansa, mallakar wani dan Labanon a yankin.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, matasa sun mamaye kamfanin wacce a baya aka sani da Madalla Floor Mill wanda ke a hanyar titin Abuja/Kaduna tun da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Talata.

An tattaro cewa sun yi nasarar shiga kamfanin ta hanyar haura katanga. An mayar da kamfanin Madalla Floor Mill zuwa dakin ajiyar kaya kwanakin baya inda yan kasuwa daga Suleja da sauran yankuna ke adana kayayyakinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel