EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya

EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya

- 'Yan Najeriya suna ta kushe da caccaka rundunar soji, tun bayan wasu sojoji sun bude wuta a Lekki Toll gate a ranar Talata

- Tukur Buratai, shugaban rundunar sojin kasa ya ce wasu 'yan ta'adda na ta tsoratar da su da yunkurin hanasu fita kasashen ketare sojoji

- A cewarsa sai da ya kai shekaru 50 kafin ya taba ketare Najeriya, don haka ba zai damu ba idan ya karasa rayuwarsa a Najeriya

Tun bayan bude wutar da sojoji suka yi a Lekki Toll gate, suka shiga tsaka mai wuya. Hakan ya faru ne tun bayan 'yan Najeriya sun fito tituna suna zanga-zanga akan rushe SARS.

A wani taro da shugaban rundunar sojin kasa, Tukur Buratai yayi a Abuja, ya zargi wasu kungiyoyi na kasashen ketare da tsoratar da sojojin da fita kasashen waje saboda zargin shiga hakkin bil'adama.

"Ya ce wasu miyagu na tsoratar da mu da hana mu kara fita kasashen ketare, amma kada mu damu, domin wajibi ne zamanmu don gyara kasarmu," cewarsa.

KU KARANTA: Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya
EndSARS: Buratai ya bayyana abinda 'yan ta'adda ke shirya wa sojin Najeriya. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

"Akaron farko da na fita kasar waje, na kai shekaru 50 kuma janar ne ni, don haka ban damu ba idan na karasa rayuwata a nan," yace.

Wasu 'yan Najeriya sun yi kira ga kasashen ketare da su dakatar da sojoji daga fita daga Najeriya sakamakon harbin masu zanga-zangar lumana da suka yi.

Buratai ya ce ba za su taba barin wani dan kasa ko kuma dan kasar waje ya cutar da kasa.

Ya ce zai cigaba da iyakar kokarinsa wurin tabbatar da zaman lafiya a kasa, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel