Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 38, sun cafke 93 a arewa maso yamma

Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 38, sun cafke 93 a arewa maso yamma

- Rundunar Operation Sahel Sanity ta bayyana ayyuka masu tarin nasarori da take yi a yankin arewa maso yamma

- Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar, ya sanar da nasarorin a wani taro da suka yi a sansani na 4 da ke Faskari

- Sun yi nasarar ceto mutum 108 da aka yi garkuwa da su, kashe wasu 38 da damke 'yan bindiga 93 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Sahel Sanity a ranar Litinin ta sanar da ayyukan da tayi a jihar Katsina da arewa maso yamma na kasar nan a cikin watanni biyu.

Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ya sanar da manema labarai ci gaban da aka samu a sansani na 4 da ke Faskari, jihar Katsina.

Sun kashe 'yan bindiga 38 tare da damke wasu 93 da miyagun makamai a cikin lokutan, The Nation ta wallafa.

An samu bindigogin toka 30, harsasai 941 da kuma alburusai 5 duk a lokacin da suka yi artabun.

Ya kara da bayyana cewa, an samu shanu 131, tumaki da raguna 154 da kuma rakumi 1. An kama mutum 90 da ake zargin da kai wa 'yan bindigar bayani tare da ceto wasu mutum 108 da aka sace.

KU KARANTA: Barna: Minista ya bayar da umarnin a kama masu kwasar kayan tallafi, a gurfanar da su

Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 38, sun cafke 93 a arewa maso yamma
Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga 38, sun cafke 93 a arewa maso yamma. Hoto daga @DefenseInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Barna: Minista ya bayar da umarnin a kama masu kwasar kayan tallafi, a gurfanar da su

A wani labari na daban, mayakan ta'addancin Boko Haram masu tarin yawa sun sheka lahira a Ngwuri Gana da ke Junacheri a jihar Borno bayan ragargazar da aka yi musu ta jiragen yaki a maboyarsu.

A wata takarda sa shugaban fannin yadaabarai na rundunar soji, Manjo Jabar John Enenche ya fitar, ya ce hakan na daga cikin kakkabar da suke yi wa 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel