Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja

Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja

- Kazamar gobara ta barke a wani bangaren sabuwar kasuwa da ke Dei-Dei a babban birnin tarayya, Abuja

- Duk da dai har yanzu ba a gane dalilin tashin mummumar gobarar ba wacce ta yi ta ruruwa

- Sai da hukumar kashe gobara suka karar da tankinsu, har suna komawa neman karikafin ta mutu

Wani bangare na sayar da kayan gine-gine dake kasuwar Dei-Dei da ke Abuja ta kama da mummumar gobara.

KU KARANTA: Yadda 'yan daba suka sace takardun makaranta na, fasfoti da kayan abinci - Dan majalisa

Bangaren, wanda aka fi sani da "Sabuwar Kasuwa" da ke tsakiyan babban birnin tarayya, Abuja shine gobarar ta lashe.

Duk da dai har yanzu ba'a gama sanin menene silar gobarar ba, amma jama'a sun tabbatar da cewa ta yi barna kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja
Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

Jami'an hukumar kashe gobara da suka zo kashe gobarar sunyi iyakar kokarinsu wurin ganin sun kashe, amma sai da suka koma domin ciko tankunan su.

Har yanzu dai babu takamaiman abinda ya kawo gobarar.

A wani labari na daban, Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Legas, Sanai (SOB) Agunbiade ya ce an biya batagarin da suka afka wa gidansa da ke Ikorodu a ranar Juma'a ne, don su kashe shi.

Agunbiade, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ikorodu ta daya, ya ce ya ji kishin-kishin cewa za'a kai masa harin, amma ya zaton duk soki burutsu ne.

Ya ce sun iso gidan amma basu sameshi ba, sai suka sace takardun makarantarsa, fasfotin tafiye-tafiyen iyalinsa da sauran abubuwa masu kima a gidansa kamar kayan abinci.

wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Tha Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel