Ku fatattaki 'ya'yanku da kayan sata idan sun kawo gida - Buhari ga iyaye

Ku fatattaki 'ya'yanku da kayan sata idan sun kawo gida - Buhari ga iyaye

- Wajibi ne duk wata mata ko kuma iyaye su mayar da yaransu ko mazansu su mayar da duk wasu kayan alatu da suka san ba za su iya siya ba cewar Buhari

- Shugaban kasar ya ce duk wani mutum mai mutunci da daraja ba zai goyi bayan masu satar dukiyar gwamnati da ta al'umma ba

- Ya ce aikin shugabannin gwamnati, na addini da na gargajiya ne taruwa wurin yaki da wannan zalama da matasa suke yi a 'yan kwanakin nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Garba Shehu, hadimin shugaban kasa, ya saki wata takarda a ranar Lahadi, inda shugaban kasa ya roki 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da su yi gaggawar tabbatar da zaman lafiya a kasa.

Shugaban kasa ya ce "Gwamnatinsa na iyakar kokarin ta na taimaka wa talakawa, mara ayyukan yi da masu kananan karfi, wadanda annobar COVID-19 ta tabarbara tattalin arzikin kasa da na jama'a. Yaja kunnen masu kai wa dukiyar gwamnati farmaki a jihohi daban-daban da ke fadin kasar nan."

A cewarsa, "Duk da kokarin gwamnatinsa na dakatar da duk wasu hanyoyin rashawa, ya yi tunanin shugabannin gwamnati, na unguwanni da na addini za su taru su yi yaki da rashawar da ke addabar kasar nan.

"Wajibi ne iyalai su umarci yaransu da su yi gaggawar mayar da duk wasu tagomashi da suka ga yaransu da shi wadanda suka san kudadensu bai isa siya masu ba, haka kuma mata su umarci mazajensu da su mayar da duk wasu kayan alatu da su ke zargin na gwamnati ne suka kwaso."

Shugaban kasa ya ce bai dace duk a ce wani mutumin kirki da zai goyi bayan satar dukiyar gwamnati ko ta al'umma, hakan zubar da kima da mutunci ne.

Ya ce sata da kwasar dukiyoyin zai kawo nakasu ga gwamnatin da ma'aikatu masu zaman kansu.

KU KARANTA: Yadda 'yan daba suka sace takardun makaranta na, fasfoti da kayan abinci - Dan majalisa

Ku fatattaki 'ya'yanku da kayan sata idan sun kawo gida - Buhari ga iyaye
Ku fatattaki 'ya'yanku da kayan sata idan sun kawo gida - Buhari ga iyaye. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun fatattaki 'yan ta'addan da suka kai hari Borno

A wani labari na daban, rayuwa ta fara komawa daidai a kananan hukumomin Jos ta Arewa da kuma Jos ta kudu awanni kadan bayan sakakullen awanni 24 a kananan hukumomin guda biyu da ke jihar Filato.

A ranar Talata ne gwamna Simon Lalong yasa kullen awanni 24 bayan rikicewar garin sakamakon zanga-zangar EndSARS da ta koma tashin hankali a kan titin Ahmadu Bello.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel