Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

- Bayan bata-gari sun fara balle ma'adanar kayayyakin tallafin COVID-19 cikin kwanakin da suka gabata, suna kwashe kayan abinci

- Cikin gaggawa gwamnonin jihohi sun fara raba kayan tallafi ba tare da jiran umarnin gwamnatin tarayya ba

- Duk da dai har yanzu ba'aji komai ba daga bakin shugaban kasa ko kuma ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa ba

Cikin gaggawa gwamnonin jihohi 36 da ke Najeriya da babban birnin tarayya Abuja sun fara rarraba kayan abincin tallafin COVID-19, ba tare da jiran umarnin gwamnatin tarayya ba.

Tun ranar Larabar da ta gabata ne bata-gari suka fara balle ma'adanar kayayyakin tallafin COVID-19 na jihohi suna kwashe kayayyakin abinci da sunan zanga-zangar EndSARS.

A cikin kwanakin da suka gabata ne jihohi suka yi ta bayar da dalilan da suka hana su raba kayan tallafin tuntuni, Daily Trust ta wallafa.

Duk da har yanzu ba a ji komai ba daga bakin shugaban kasa da ma'aikatar jinkai da walwalar 'yan kasa ba, a kan ko sun san cewa gwamnatin jihohi basu raba kayan tallafin ba.

Dama mutane da dama sun yi ta caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin APC akan kayan tallafin da sukace sun bayar a raba wa 'yan Najeriya.

Ba Buhari kadai ba, hatta ministan tallafin da jin kai ba a barta ta huta ba da kalubale.

KARANTA: Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su bi doka - NSA

Tallafin korona: FG ta wanke kanta, ta sanar da umarnin da ta bai wa gwamnoni
Tallafin korona: FG ta wanke kanta, ta sanar da umarnin da ta bai wa gwamnoni. Hoto daga @Dailytrust
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za su kalmashe kafa suna kallon 'yan ta'adda suna cin karensu babu babbaka ba a Najeriya.

Ya fadi hakan ne a taron da yayi da tsofaffin shugabannin kasa kamar su Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Ernest Shonekan, janar Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel