Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

- Wasu masu garkuwa da mutane sun kashe SB Onifade, babban soja mai mukamin Kanal a rundunar sojin Najeriya

- Masu garkuwa da mutanen sun kashe Kanal Onifade bayan karbar kudin fansa har Naira miliyan goma

- Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wajen sace mutane tare da yin garkuwa dasu duk da jami'an tsaron da ke sintiri a titin

Rahotanni da Legit.ng Hausa ta samu sun bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kashe SB Onifade, babban soja mai mukamin Kanal a rundunar sojin Najeriya.

Masu garkuwa da mutane sun kashe Kanal Onifade bayan karbar kudin fansa har Naira miliyan goma.

Masu garkuwa da mutane sun sace Kanal Onifade, kwararren likita, a daura da kamfanin kayan noma na 'Olam' da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren ranar 27 ga watan Satumba.

KARANTA WANNAN: Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m
Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m - Peoples Gazettes
Asali: UGC

Daily Nigerian ta rawaito cewa rundunar soji ta tura wata tawaga mai karfi domin kubutar da Kanal Onifade duk da suna tattauna biyan kudin fansa da 'yan ta'addar da suka sace shi.

Jaridar ta bayyana cewa majiyarta ta tabbatar mata da cewa masu garkuwa da mutane sun kashe Kanal Onifade a daren ranar Asabar bayan iyalinsa da 'yan uwansa sun biya miliyan goma kudin fansa.

KARANTA WANNAN: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola

Kokarin Daily Nigerian na jin ta bakin kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, bai yiwu ba saboda bai samu danar amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wajen sace mutane tare da yin garkuwa dasu duk da jami'an tsaron da ke sintiri a titin.

A watan Afrilu na shekarar 2019 ne babban sifeton rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya kaddamar da rundunar atisayen 'Puff Adder' domin magance garkuwa da mutane da sauran aiyukan ta'addanci a jihohin Kogi, Katsina, Niger, da Zamfara.

Bayan kaddamar da atisayen, an baza dumbin jami'an 'yan sanda a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna domin tabbatar da tsaron lafiyar matafiya.

A wani labarin, Mayakan ta'addancin Boko Haram masu tarin yawa sun sheka lahira a Ngwuri Gana da ke Junacheri a jihar Borno bayan ragargazar da aka yi musu ta jiragen yaki a maboyarsu.

A wata takarda sa shugaban fannin yadaabarai na rundunar soji, Manjo Jabar John Enenche ya fitar, ya ce hakan na daga cikin kakkabar da suke yi wa 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel