EndSARS: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata

EndSARS: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata

- Kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin 'yan sanda yayi magana a kan EndSARS

- Shugaban kwamitin ya bukaci a biya diyya ga 'yan sanda da farar hula da suka rasa rayukansu

- IGP ya ce 'yan sandan Najeriya sun mayar da hankali wurin tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar

Kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin 'yan sanda ya ce akwai bukatar a biya diyya ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar EndSARS.

An yi zanga-zanga a fadin kasar nan a kan cin zarafi da zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan, lamarin da ya zarta mako daya.

'Yan Najeriya sun bi tituna inda suke bukatar a gyara ayyukan 'yan sanda amma sai zanga-zangar ta koma wani abu daban.

KARANTA WANNAN: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

EndSARS: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata
EndSARS: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata - @thecableng
Asali: Twitter

A yayin jawabi a taron, Mohammed Adamu, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Shugaban kwamitin, Usman Bello Kumo, sun ce diyyar za ta kasance ga 'yan sanda ne da kuma farar hula da suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu.

Kumo ya ce akwai bukatar a fitar da sunayen wadanda suka rasa rayukansu da kuma kadarorin sa aka rasa.

"Muna bukatar bayani a kan 'yan sanda da suka rasu ko kuma aka ci zarafinsu a kwanakin da suka gabata da kuma kadarorin da aka rasa," dan majalisar wanda ya samu rakiyar abokan aikinta ya sanar.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ya ki magana a kan harbin Lekki - Fadar shugaban kasa

Shugaban kwamitin ya kara da mamakin yadda 'yan sanda basu jagoranci tabbatar da dokar kulle a Legas ba amma sai sojoji.

"A yanzu da aka rushe rundunar y, menen matakan da aka dauka domin tabbatar da kwarewar SWAT?" Ya tambaya.

A bangaren daya, Adamu ya ce sun fara duba lamarin da yasa aka yi zanga-zanga da kuma dalilin da tarzoma ta biyo baya.

IGP ya ce 'yan sanda sun mayar da hankali wurin gyara da kuma tabbatar da cewa babu wani tashin hankali a ko ina.

A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a yanzu.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya saki a ranar Juma'a a Abuja.

Ologbondiyan ya ce sun dauki wannan matakin ne don nuna alhininsu a kan kisan matasa da aka yi a Lekki Toll Gate da sauran kashe-kashe da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel