EndSARS: Kowa ya je jiharsa ya wanzar da zaman lafiya - Buhari ya umurci ministocinsa

EndSARS: Kowa ya je jiharsa ya wanzar da zaman lafiya - Buhari ya umurci ministocinsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci gaba daya ministocinsa da su koma jihohinsu na haihuwa domin gudanar da wani babban aiki.

- Ana sa ran ministocin za su gana da masu ruwa da tsaki na jihohinsu domin dakatar da zanga-zangar #EndSARS da kuma wanzar da zaman lafiya

- Ministan albarkatun ruwa Sulaiman Adamu, ya tabbatar da hakan a ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministocinsa da su koma jihohinsu na haihuwa domin kwantar da tarzomar masu zanga zangar #EndSARS da kuma wanzar da zaman lafiya.

Ana sa ran ministocin za su gana da masu ruwa da tsaki na jihohinsu domin zayyana masu kokarin gwamnatin tarayya na cika buri da bukatun matasan.

Ministan albarkatun ruwa Sulaiman Adamu, ya tabbatar da hakan a ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce an umurci ministocin da su koma jihohinsu, domin taimakawa shuwagabannin siyasa, masu rike da sarautun gargajiya da na addinai, don kawo karshen zanga zangar #EndSARS.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ya ki magana a kan harbin Lekki - Fadar shugaban kasa

EndSARS: Kowa ya je jiharsa ya wanzar da zaman lafiya - Buhari ya umurci ministocinsa
EndSARS: Kowa ya je jiharsa ya wanzar da zaman lafiya - Buhari ya umurci ministocinsa - @NGRPresident
Asali: Twitter

Adamu ya ce ya je jihar ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin wanzar da zaman lafiya da kuma rubuta rahoto don kaiwa shugaban kasa Buhari cikin gaggawa.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman goyon bayan dukkanin shuwagabannin siyasa a jihohin da su dakatar da al'umarsu daga aikata laifukan da za su kawo rabuwar kai.

Ministan harkokin Niger Delta Godswill Akpabio wanda ya je Akwa Ibom a Uyo a ranar Asabar, ya samu rakiyar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin Niger Delta, Sanata Ita Enang.

KARANTA WANNAN: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS

Ya bukaci matasan jihar da su rungumi zaman lafiya kasancewar shugaban kasa Buhari ya dukufa wajen cika masu burinsu na yin garambawul a rundunar 'yan sandan Nigeria.

Akpabio ya ce gwamnati na iya bakin kokarinta wajen samar da ayyukanyi, bunkasa al'umma da kuma farfado da tattalin arziki a jihar da ma shiyyar Niger Delta ba ki daya.

Ya ce zanga zangar EndSARS da ta dauki wani sabon salo, na iya razanar da masu saka jari su tsere, hakan zai kawo babbar koma baya ga jihar da ma kasar baki daya.

A wani labarin, wasu mutane da ake zargin 'yan daba suka tsinke kan dan sanda tare da kone shi kurmus yayin zanga-zangar EndSARS a Nnewi da ke jihar Anambra.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu 'yan sandan uku sun samu miyagun raunika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel