Dalilin da yasa Buhari ya ki magana a kan harbin Lekki - Fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar sa dalilinta na yin shiru a kan harbe-harben Lekki
- Mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina ya sanar da dalilin
- Ya ce zai zama tamkar riga Malam masallaci ne domin ba a kammala bincike a kan lamarin ba
Shugaban masa Muhammadu Buhari bai ce komai a man harbe-harben da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki a ranar Talata ba a jawabin da yayi ga 'yan Najeriya saboda baya son yayi riga Malam masallaci.
Da yawa daga cikin 'yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan rashin maganar shugaban kasan ko jaje ga jama'ar da suka rasa rayukansu. Sun kwatanta hakan da ganganci da kuma rashin nuna kulawa.
KARANTA WANNAN: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS

Asali: Twitter
Amma kuma, mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina, wanda ya bayyana a shirin siyasarmu a yau a gidan talabijin na Channels, ya ce shugaban kasan bai samu cewa komai a kan harbin ba saboda ba a kammala bincike a kai ba.
KARANTA WANNAN: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara
Ya ce: "Hedkwatar tsaro ta fitar da takarda inda tace tana bincikar lamarin. Gwamnan jihar Legas ya kafa kwamitin bincike a kan abinda ya faru.
"Toh don haka shugaban kasan bashi da ta cewa saboda zai zama tamkar riga Malam masallaci ne a kan binciken da ake yi. Bayan binciken ne zai yanke hukuncin magana a kai."
A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a yanzu.
Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya saki a ranar Juma'a a Abuja.
Ologbondiyan ya ce sun dauki wannan matakin ne don nuna alhininsu a kan kisan matasa da aka yi a Lekki Toll Gate da sauran kashe-kashe da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS.
Dama da safiyar Alhamis jam'iyyar PDP ta umarci a kwantar da tutocin ta da ke kowanne ofishi a fadin kasar nan saboda lokacin nan mai cike da kalubale.
PDP ta roki INEC ta dage zabuka 15 da aka shirya yi a ranar 31 ga watan Oktoba a kasar nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng