Da duminsa: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS

Da duminsa: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS

- PDP ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa da na jam'iyya sakamakon kashe-kashen matasa dalilin zanga-zangar EndSARS

- A cewar Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Kola Ologhondiyan, wajibi ne su dakatar da komai saboda tashin hankalin da Najeriya take ciki

- A cewarsa, sun roki INEC da ta taimaka ta matsar da zaben da za'ayi ranar 31 ga watan Oktoba zuwa lokacin da aka samu zaman lafiya

Jam'iyyar PDP ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a yanzu. Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya saki a ranar Juma'a a Abuja.

Ologbondiyan ya ce sun dauki wannan matakin ne don nuna alhininsu a kan kisan matasa da aka yi a Lekki Toll Gate da sauran kashe-kashe da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS.

KARANTA WANNAN: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara

Da duminsa: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS
Da duminsa: PDP ta dakatar da ayyukan siyasa da shirin zabe saboda #EndSARS - @vanguardngr.com
Asali: UGC

Dama da safiyar Alhamis jam'iyyar PDP ta umarci a kwantar da tutocin ta da ke kowanne ofishi a fadin kasar nan saboda lokacin nan mai cike da kalubale.

PDP ta roki INEC ta dage zabuka 15 da aka shirya yi a ranar 31 ga watan Oktoba a kasar nan.

KARANTA WANNAN: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

NAN ta sanar da cewa, a ranar Laraba, INEC ta sanar da dage zabukan sanatoci 6 da kuma na mazabu 9 a jihohi 11.

INEC ta ce za ta cigaba da duban yanayin lafiyar kasa da kwanciyar hankali don samar da lokacin da za'a yi zabukan cikin sati 2.

PDP ta yi kira ga 'yan Najeriya, da su kwantar da hankulan su, kuma su cigaba da addu'a har mafita ta samu, don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya.

A kokarin dakarun sojin saman Najeriya na jaddada zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso gabas na kasar nan, rundunar Operation Wutar Tabki na cigaba da samun nasarori.

Samamen kwanan nan da dakarun sojin suka kai ya matukar girgiza mayakan ISWAP, sansaninsu da wuraren adana makamai da ke Tumbun Barorowa a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel