EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari

EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai kalmashe kafa yana kallon kuda kwado yayi masa kafa ba

- Ya ce zai tabbatar ya kawo karshen ta'addanci, rikici da tashin hankali a Najeriya, sai dai zai tabbatar da adalci ga 'yan Najeriya

- Ya fadi hakan ne a wani taro da yayi da tsofaffin shugabannin Najeriya, irinsu Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za su kalmashe kafa suna kallon 'yan ta'adda suna cin karensu babu babbaka ba a Najeriya.

Ya fadi hakan ne a taron da yayi da tsofaffin shugabannin kasa kamar su Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Ernest Shonekan, janar Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.

Shugaban kasa yace abin kaico ne ace daga manufar matasa ta rushe rundunar SARS ta koma tashin hankali da rikici, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce asalin abinda ya janyo zanga-zangar shi ne kama-karyar da wasu daga cikin 'yan rundunar SARS ke yi, wanda suka bukaci a rushe rundunar kuma aka yi.

Shugaban kasa yace, "Mun amince da bukatunsu amma sun cigaba da zanga-zangar wacce ta janyo zubar da jini."

KU KARANTA: Alkali ya bukaci mahaifi ya yi wa diyarsa addu'a bayan ya maka ta a kotu

EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari
EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

Kamar yadda kakakin shugaban kasar ya ce a wata takarda, abinda ya fi tada masa hankali shine kashe-kashe da asarorin dukiyoyin gwamnati da na al'umma.

Shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya a ranar Alhamis, inda yace "Za mu cigaba da inganta mulki don samar da rayuwa mai kyau ga 'yan kasa.

"Za mu cigaba da tabbatar da bai wa matasa dama, taimakon 'yan Najeriya da basu 'yancin su. Zamu cigaba da tabbatar da hadin kan 'yan kasa," cewar shugaban kasa.

A wani labari na daban, A ranar juma'a, 23 ga watan Oktoba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taro da tsofaffin shugabannin kasar Najeriya don neman yadda za'a bullowa zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici.

Shugaba Buhari ya sanar da tsofaffin shugabannin kasar asalin dalilin da ya janyo zanga-zangar matasa ta EndSARS, wacce daga baya ta koma tashin hankali, Legit.ng ta gano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel