Ba yadda suka iya: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara

Ba yadda suka iya: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara

- Wani abun al'ajabi ya faru a ranar Juma'a, inda dandazon mutane suka balle babban dakin ajiyar kaya, suka kwashe kayan tallafin COVID-19

- Babban abun mamakin shine, yadda mutanen suka yi warwason kayan a gaban jami'an tsaro, ba tare da sun tanka masu ba

- Sai dai, gwamnatin jihar Kwara, jihar da lamarin ya faru, ta yi Allah wadai da wannan mummunar dabi'a ta satar 'kayan da ba naka ba'

A ranar Juma'a, wasu dandazon jama'a suka balle wani babban dakin ajiya, inda suka kwashe kayan tallafin annobar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

An boye kayan ne a babbar tashar jirgin sama na kasa da kasa da ya ke Ilorin, jihar Kwana, a bangaren ajiye kayayyaki na manyan jirage.

Mutanen sun balle kofar shiga bangaren inda suka bude babban dakin ajiyar kayan tallafin da tsakiyar rana, yayin da jami'an tsaro ke kallonsu, ba tare da yin wani abu ba.

KARANTA WANNAN: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki zaman lafiy

Ba yadda suka iya: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara
Ba yadda suka iya: Jami'an tsaro na kallo mutane suka sace tallafin COVID-19 a Kwara @OJay_Jahswill
Asali: Twitter

Sun samu nasarar wawushe komai na kayan abinci da ke a cikin babban dakin ajiyar, amma suka fara gudun ceton rai, bayan da suka jiyo jiniyar jami'an tsaro na isowa wajen.

A jawabinta kan lamarin, gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da wannan mummunar dabi'a ta satar kayan tallafi da jama'ar suka yi.

Kwamishinan sadarwa a Kwara, Harriet Afolabi-Oshatimehin, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa, an ajiye kayan tallafin ne domin rabawa talakawa.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas

Ta jaddada cewa irin wannan mummunar dabi'ar da mutanen suka nuna, ba ta yi kama da kyakkyawar dabi'ar mutanen jihar ba.

A cewar Afolabi-Oshatimehin, kwamitin raba tallafin COVID-19 a jihar tuni ya raba mafi akasarin kayan tallafin da aka kawo, kuma akalla kananan hukumomi 15 suka amfana da wannan rabo.

Sauran ragowar kayan tallafi da bata garin suka yi awon gaba da shi, an ajiye shi ne domin rabawa karamar hukumar da tayi saura da kuma gajiyayyu marasa galihu.

A wani labarin na ranar Alhamis, wasu mutane da ake zargin 'yan daba suka tsinke kan dan sanda tare da kone shi kurmus yayin zanga-zangar EndSARS a Nnewi da ke jihar Anambra.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu 'yan sandan uku sun samu miyagun raunika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel