Dalla-dalla: Bayanin taron Buhari da tsoffin shugabannin kasa

Dalla-dalla: Bayanin taron Buhari da tsoffin shugabannin kasa

- A ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba, Shugaba Muhammadu Buhari ya tara duk tsofaffin shugabannin kasa masu rai don neman yadda za'a shawo kan rikicin EndSARS

- Kamar yadda mai ba shugaban kasar shawara a harkar labarai, Femi Adesina ya sanar a wata takarda, ya ce Buhari ya sanar da tsofaffin shugabannin kasar dalilin fara rikicin

- Ya sanar da su cewa matasan sun bukaci a rushe SARS, a biya diyyar gawawwaki, da sauran bukatu kuma duk ya amince amma sun cigaba da zanga-zangar

A ranar juma'a, 23 ga watan Oktoba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taro da tsofaffin shugabannin kasar Najeriya don neman yadda za'a bullowa zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici.

Shugaba Buhari ya sanar da tsofaffin shugabannin kasar asalin dalilin da ya janyo zanga-zangar matasa ta EndSARS, wacce daga baya ta koma tashin hankali, Legit.ng ta gano.

Mun samu wannan labarin ne a wata takarda da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkar labarai, Femi Adesina, ya saki.

Buhari ya ce ba zai nade kafa yana kallon kasarsa cike da tarzoma, tashin hankali, ta'addanci da rikici irin wannan ba.

A cikin taron wanda duk tsoffin shugabannin kasa masu rai halarta, irin Janar Yakubu Gawon, Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Ernest Shonekan, janar Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.

Buhari ya sanar da su matakan da ya dauka yayin da matasan suka zo masa da bukatar rushe SARS, kuma ya amince da hakan.

Suka kuma bukaci ya saki duk wasu matasa da aka kama. Sannan a yi adalci ga duk wadanda 'yan sanda suka kashe sakamakon zanga-zangar, a biya danginsu diyya.

Ya ce sun bukaci a bayar da gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu cikin kwanaki 10, sannan a tabbatar an duba lafiyar kwakwalwar jami'an SARS da aka rushe kafin a kara daukarsu wani aiki. Matasan sun bukaci a kara albashin 'yan sanda.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa duk ta amince da bukatunsu amma kuma sun cigaba da zanga-zangar, wanda hakan ya bashi mamaki.

KU KARANTA: Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

Dalla-dalla: Bayanin taron Buhari da tsoffin shugabannin kasa
Dalla-dalla: Bayanin taron Buhari da tsoffin shugabannin kasa. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta yi kira ga duk wasu masu fadi aji a kasar nan da su yi kokarin saka baki akan wannan zanga-zangar ta EndSARS da ke ta kara ruruwa a kasar nan.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi wannan kiran ne bayan sun samu labari a kan irin tabarbarewar tsaro da ke kara yawa sakamakon zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel