Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su bi doka - NSA

Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su bi doka - NSA

- Jami'an tsaro suyi iyakar kokarin su wurin tsayawa daidai dokar da shari'a ta tanadar wurin kwantar da tarzoma, cewar Buhari ga jami'an tsaro

- Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya sanar da manema labarai hakan a ranar Alhamis

- A cewarsa, shugaban kasa ba zai so ya dinga ganin tashin hankali, asarar dukiya da kuma zubar da jini a kasarsa ba

A ranar Alhamis ne mai bayar da shawara ga shugaban kasa akan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, yace shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce jami'an tsaro su yi aiki daidai iyakar da shari'a ta tsayar da su wurin shawo kan rikicin da ke faruwa a Najeriya.

Monguno ya bayyana hakan ne yayin da manema labaran gidan gwamnati suka yi hira da shi bayan gama taron jami'an tsaro da shugaban kasa ya shirya.

Ya ce duk da gwamnati ta yi abinda masu zanga-zangar ke bukata, kamar yadda aka gani zanga-zangar ta canja salo mara kyau.

Yace shugaban kasa baya fatan ganin ana tashin hankali da kashe-kashe a kasarsa, The Punch ta sanar.

Ya kara da cewa, "Don haka, ya umarci duk jami'an tsaro su yi iya kokarin ganin sun tsaya a iyakokin shari'a, kada su yi wani abu da zai kara lalata al'amura."

KU KARANTA: Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su bi doka - NSA
Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su bi doka - NSA. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Akwai yuwuwar mu sassauta dokar kulle a ranar Juma'a - Sanwo-Olu

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 24, mai suna Abdulateef Yusuf Bamidele, a babban birnin tarayya, Abuja.

Al'amarin ya faru da safiyar Juma'a a Guidna, Kubwa, wata anguwa dake kusa da Bwari a Abuja. Guidna ba ta da nisa da sansanin masu bautar kasa na Abuja.

A hirar da The Cable suka yi da mahaifiyar Bamidele, tace masu garkuwa da mutanen sun zo gidansu da misalin karfe 1:25 na dare bayan sun hauro ta katanga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel