EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

- Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da tsinke wa wani dan sanda kai kuma aka banka masa wuta

- Hakan ta faru sakamakon harin da wasu 'yan daba masu zanga-zanga suka kai ofishinsu da ke Nnewi

- Kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar da mutuwar wasu mutum uku cikin biyar a asibitin garin

A ranar Alhamis ne wasu mutane da ake zargin 'yan daba suka tsinke kan dan sanda tare da kone shi kurmus yayin zanga-zangar EndSARS a Nnewi da ke jihar Anambra.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu 'yan sandan uku sun samu miyagun raunika.

Ya ce an gaggauta mikasu asibiti domin samun taimakon likitoci na gaggawa, The Nation ta ruwaito.

Ya ce an an kai wa wasu mutum biyar hari a Onitsha kuma an kai su asibiti inda ake kula da su amma uku daga cikinsu sun rasu.

KU KARANTA: EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar

EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra
EndSARS: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra. Hoto daga @TheNation
Asali: UGC

KU KARANTA: Fursunoni sun bankawa gidan yari wuta a Warri, da dama sun tsere duk da harbe-harben jami'an tsaro

Ya kara da bayyana cewa, masu zanga-zangar sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke Nnewi, sun banka masa wuta tare da kone motocin sintiri.

Kamar yadda yace, "A ranar 21 ga watan Oktoba wurin karfe 11:30 na dare, 'yan daba masu tarin yawa da suka fake da zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke Nnewi, sun banka masa wuta tare da kone ababen hawa na sintiri. Sun kwashe makamai masu yawa.

"Hakazalika, a ranar 22 ga watan Oktoban 2020 tsakanin karfe 3:30 na safe zuwa 5 na yamma, sun kashe dan sanda daya sannan suka banka masa wuta. Wasu ukun sun samu miyagun raunika amma an garzaya da su asibiti."

A wani labari na daban, Ministan Abuja, Muhammadu Bello, a ranar Alhamis, ya bayyanar da yadda suka tsara wata kwamiti da za ta tabbatar da biyan ababen hawa da kuma abubuwan da aka yi asara.

Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis bayan ya kai ziyara ga Apo Mechanic Village da Dutse Alhaji da ke kusa da Bwari bayan rikicin EndSARS ya barke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel