Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

- Wannan satin ya kasance mai matukar tarihi a kasar Najeriya gaba daya

- Masu zanga-zangar EndSARs sun zarce da kashe-kashe tare da kone-kone wanda ya koma tarzoma

- Adesina ya ce ko nan gaba Najeriya ta tarwatse, toh babu shakka kiyayya ce ta tarwatsa ta

Wannan mako ne mai cike da tarihi a kasar nan. A cikin watan nan ne Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya horemu da mu zauna lafiya tare da hada kai da kuma mantawa da tsohuwar gaba wacce ke kawo rikici.

Abinda ya fara tamkar zanga-zangar lumana daga wasu matasan Najeriya a kan cin zarafin da rundunar ta musamman ta yaki da fashi da makami ke yi a Najeriya, ya koma wani abu na daban da ya kawo kashe-kashe da rikici.

Tunanina da ta'aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

KU KARANTA: PDP ta shigar da karar INEC da Gbajabiamila bayan jigo a jam'iyyar ya koma APC

Wasu jama'a suna alakanta hakan da kuskuren 1914 wanda aka hada yankin arewaci da kudanci har aka samu Najeriya. Tun daga nan alakar ta kasa zama guda daya tsakanin yankunan. Wutar kiyayya ta cigaba da ruruwa.

Idan har Najeriya ta tarwatse, ko yanzu ko a nan gaba, babu shakka kiyayya ce ta kawo hakan. Ta yaya jama'a za su cigaba da daukar gaba suna amfani da ita wurin kashe junansu, tarwatsa shugabanci da kuma hana zaman lafiya?

"Idan muka rasa wa za mu ki, sai mu fara kin kanmu," wani marubuci yace.

Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina
Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina. Hoto daga @FemAdesina
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar

A wani labari na daban, Ministan Abuja, Muhammadu Bello, a ranar Alhamis, ya bayyanar da yadda suka tsara wata kwamiti da za ta tabbatar da biyan ababen hawa da kuma abubuwan da aka yi asara.

Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis bayan ya kai ziyara ga Apo Mechanic Village da Dutse Alhaji da ke kusa da Bwari bayan rikicin EndSARS ya barke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel