Yadda jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce daga jama'a

Yadda jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce daga jama'a

- Jawabin kai tsaye da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jiya ya jawo cece-kuce da dama a kafafen sada zumuntar zamani

- Bayan shugaban kasar ya yi jawabi a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 'yan gwagwarmaya daga kasashen ketare da na cikin gida sunyi ta sukar jawabin

- Inda suke cewa, sun dade suna jiran jawabi sai dai kuma, da yin jawabin gara rashinsa, don bai tabo abubuwa da dama masu muhimmanci ba

Jawabin kai tsaye da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba ya kawo cece-kuce.

Inda wasu ke ganin cewa ya bar baya da kura, akwai batutuwa da dama da yakamata a ce ya yi magana a kansu amma bai yi ba.

A watan Oktoban 2020 ne karo na farko da shugaban kasa yayi jawabi sau 3 a cikin wata daya, inda yayi a ranar 1, 12 da kuma 22 duk a cikin watan Oktoba.

Shugaban kasa ya yi gargadi a kan zanga-zangar EndSARS da su kiyaye, kuma su tabbatar sun yi ta a lumana babu tashin hankali.

Kwanakin baya manyan 'yan gwagwarmaya daga kasashen ketare da manyan mutane sun fito fili sun caccaki shugaban kasar, a daidai lokacin da Najeriya take cikin tsanani.

KU KARANTA: Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

Yadda jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce daga jama'a
Yadda jawabin shugaba Buhari ya janyo cece-kuce daga jama'a. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: FG ta kara tura dakarun soji domin tsare kayan gwamnati a Legas

Wani dan Najeriya da yake aikin jaridanci a Amerika mai suna Farooq Kperogi, ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yace shugaban kasar bai yi magana a kan kashe-kashe da aka yi a Lekki ba, da kuma ta'adin da 'yan ta'adda suka yi kwanan nan a kauyen Tungar da Talatar-Mafara dake jihar Zamfara ba.

Sai kuma wani shagube da tsohon Sanata wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani yayi, inda yace 'yan Najeriya sun bukaci Buhari yayi jawabi kuma ya yi, gashi sun rasa abinda za su fada.

Sai kuma wata wallafa da jam'iyyar adawa ta PDP tayi, inda ta nuna rashin gamsuwarta karara a kan jawabin shugaban kasar a shafinta na Twitter, inda tace abin ban haushi da takaici ne yadda aka jima ana jiran jawabi sai kuma aka ji na jiya.

A wani labari na daban, Majalisar dattawa ta yi kira ga duk wasu masu fadi aji a kasar nan da su yi kokarin saka baki akan wannan zanga-zangar ta EndSARS da ke ta kara ruruwa a kasar nan.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi wannan kiran ne bayan sun samu labari a kan irin tabarbarewar tsaro da ke kara yawa sakamakon zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel