'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja

'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja

- Masu garkuwa da mutane sun amshe kudade kuma suka dauke wani saurayi, Abdulateef Yusuf Bamidele, dan shekara 24 a Abuja

- Sun je har gidansu Bamidele wuraren Bwari inda suka kasa tafiya da mahaifiyarsa suka tafi da shi

- A hirar da aka yi da mahaifiyar Bamidele, ta shaida musu cewa da misalin karfe 1:25 na dare suka shigo gidan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 24, mai suna Abdulateef Yusuf Bamidele, a babban birnin tarayya, Abuja.

Al'amarin ya faru da safiyar Juma'a a Guidna, Kubwa, wata anguwa dake kusa da Bwari a Abuja. Guidna ba ta da nisa da sansanin masu bautar kasa na Abuja.

A hirar da The Cable suka yi da mahaifiyar Bamidele, tace masu garkuwa da mutanen sun zo gidansu da misalin karfe 1:25 na dare bayan sun hauro ta katanga.

Matar tace, bayan amsar kudade sai da suka dauke Bamidele.

"A lokacin da suka zo, sun yi mana magana ta taga, inda suka ce idan bamu bude musu kofa ba, za su yi mana rashin mutunci," a cewarta.

KU KARANTA: EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja
'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa

"Bayan mun bude musu kofa ne suka ce mu fito da kudi, muka basu cinikin kwana biyu da muka yi, sai suka ce ya yi kadan."

Ta ce masu garkuwa da mutanen sun so su tafi da ita, amma basu samu dama ba, sai suka tafi da danta.

"Sun so dauka ta, amma na kasa haura katanga, sai suka dawo suka dauki da na," cewarta.

Da aka tambayi kakakin 'yan sanda, Miriam Yusuf, ta ce suna sane da faruwar lamarin, kuma suna iya kokarinsu na ganin sun ceto shi.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, ya bayyana ranar da zai cire kullen da yasa a jihar Legas.

A wata hira da gidan talabijin din Arise suka yi da gwamnan, ya ce za'a cigaba da shige da fice a jihar daga ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel