EndSARS: FCT za ta biya ababen hawa da gine-ginen da aka lalata - Minista

EndSARS: FCT za ta biya ababen hawa da gine-ginen da aka lalata - Minista

- Abuja garinmu ne, kuma garinku ne, ku da kuka zo neman na tuwo, cewar ministan Abuja yayin da yaje jaje ga wadanda asara ta shafa

- Ministan Abuja, Muhammadu Bello, ya ja kunnen mazauna Abuja a kan zanga-zangar EndSARS da ta koma tashin hankali

- Inda yace su kwantar da hankalinsu, sun samar da kwamitin da za ta tabbatar da biyan duk wata asara da aka yi

Ministan Abuja, Muhammadu Bello, a ranar Alhamis, ya bayyanar da yadda suka tsara wata kwamiti da za ta tabbatar da biyan ababen hawa da kuma abubuwan da aka yi asara.

Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis bayan ya kai ziyara ga Apo Mechanic Village da Dutse Alhaji da ke kusa da Bwari bayan rikicin EndSARS ya barke.

"Kada ku bar wasu bare su raba mu. Hukumar birnin tarayya ta samar da wani kwamiti wanda zai tabbatar da biyan ababen hawa da kuma sauran kayan da aka yi asara sakamakon zanga-zangar EndSARS," a cewarsa.

Ya shawarci 'yan Najeriya da kada su biye wa bare su raba kawunan su, Daily Nigerian ta wallafa.

"Wajibi ne mu hada kai mu zauna lafiya. Na zo ne don yi muku jaje, akwai kwamitin da aka samar don biyan wadanda asara ta same su.

"Abuja garinmu ne, da ku da ku ka zo neman na tuwo. Don haka babu wani dalilin da zai sa mu yarda wasu su rabamu." ya kara da cewa.

KU KARANTA: Kalaman Fafaroma Francis a kan auren jinsi zasu jawo ma sa suka a duniya

EndSARS: FCT za ta biya ababen hawa da gine-ginen da aka lalata - Minista
EndSARS: FCT za ta biya ababen hawa da gine-ginen da aka lalata - Minista. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo

A wani labari na daban, a cikin wani faifan bidiyo da ya yi farin jini a dandalin sada zumunta, an ga sojojin Najeriya na lallaba matasa ma su zanga-zanga a jihar Legas.

A daren ranar Talata ne wasu kafafen yada labari na gida da ketare suka wallafa rahoton cewa dakarun soji sun budewa ma su zanga-zanga a yankin Lekki na jihar Legas wuta.

Sai dai, a cikin faifan bidiyon da aka nada ranar Laraba yayin zanga-zanga a jihar Legas, an ji sojoji suna huduba cikin lafazi mai dadi ga matasan da ke zanga-zanga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel