Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa

- Wani dan Najeriya mai suna Sorarex, ya ce daga yau zai sauka daga matsayin shugaban gidansa

- Dan kasuwan ya ce, zai sa matarsa ta maye gurbinsa saboda yanayin yadda rayuwa ta koma

- Ya fadi hakanne sakamakon yadda matsalolin rayuwa ke karuwa kullum shiyasa ya dauki wannan matakin

Wani dan Najeriya mai suna Sojarex, ya sanar da yadda rayuwar gidansa ta kasance a kafar sada zumuntar zamani.

A wata wallafa da Sojarex yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, dan kasuwar ya ce yana tunanin sauka daga matsayinsa na shugaban gidansa, saboda matsalolin harkar iyali, ya bai wa matarsa damar shugabantarsa da yaransu.

Kamar yadda ya wallafa: "Sakamakon yadda matsaloli ke kara yawaita a gidana da halin rayuwa a yanzu, zan sauka daga shugabancin gidana. Matata za ta maye gurbina daga yanzu. Nagode kuma Allah yayi muku albarka."

KU KARANTA: EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa
Magidanci ya nada matarsa shugaba a gidansa, ya ce matsalolin gidansa sun yi yawa. Hoto daga @sojarex_ / Instagram
Asali: Instagram

KU KARANTA: EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato ya yi taro da shugabannin gargajiya a gidan gwamnatin Filato don kawo karshen tarzomar da ta barke a jihar, Pemium Times ta wallafa hakan.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya cewa shugabannin gargajiya, su zai kama da laifi matsawar ba'a samu kwanciyar hankali ba a jiharsa sakamakon zanga-zangar rushe SARS.

NAN ta ruwaito yadda Lalong ya saka kulle a kananan hukumomin arewa da kudancin Jos a ranar Talata.

Bayan faruwar hakan ne al'amarin ya kazanta, inda matasa suka yi ta asarar rayuka.

Lalong yace, "Ina umartar ku da ku yi gaggawar daukar matakan da suka dace don kawo karshen tarzomar nan da ta barke a yankunan ku.

"Gwamnati za ta kama ku da laifi matsawar baku dauki matakin da ya dace ba.

"Ku yi kokarin tara matasa ku nuna musu fushinku akan al'amuran da ke faruwa don samun maslaha."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel