Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 4, sun samo manyan bindigogi 4 a Borno - DHQ

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 4, sun samo manyan bindigogi 4 a Borno - DHQ

- Rundunar Operation Lafiya Dole na cigaba da ragargazar 'yan Boko Haram ta jirgin sama da kuma kasa a jihar Borno

- Kakakin rundunar soji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin gabatar da jawabi a kan nasarorin rundunar

- Ya ce harin da rundunar suka kai tsakanin 15 zuwa 21 ga watan Oktoba, sun samu nasarar ragargazar 'yan Boko Haram da amshe makamansu da dama

Hedkwatar tsaro tace Operation Lafiya Dole ta samu nasarar ragargazar 'yan Boko Haram 4, kuma ta kwace bindigogi AK47 a hannunsu, yayin da suka je aiki kauyen Sawa dake karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan yayin da yake bayar da bayani a kan ayyukan da rundunar suka yi a ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa, rundunar Operation Lafiya Dole ta sama da kasa sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'adda da dama da ke maboyarsu cikin sati daya a Arewa maso gabas.

Enenche ya ce, rundunar ta yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'adda tsakanin 15 zuwa 21 ga watan Oktoba.

Ya ce rundunar ta musanta labaran da ake yi a kan yawon da 'yan Boko Haram ke yi yadda suka ga dama, hasali ma sai dai rashin walwalar da suka sa wa 'yan ta'addan.

Ya ce harbin da rundunar sojin sama suka yi a ranar 15 ga watan Oktoba, sun samu nasarar ragargazar 'yan Boko Haram da maboyarsu da ke Kauyukan Tudun Wulgo da Tumbun Gini kusa da tafkin Chadi.

KU KARANTA: EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 4, sun samo manyan bindigogi 4 a Borno - DHQ
Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 4, sun samo manyan bindigogi 4 a Borno - DHQ. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Akwai yuwuwar mu sassauta dokar kulle a ranar Juma'a - Sanwo-Olu

A wani labari na daban, Don gujewa cigaba da asarar dukiyar gwamnati a jihar Legas, gwamnatin tarayya ta kara yawan jami'an tsaro don kula da dukiyoyin gwamnati da ke jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a safiyar Alhamis, yayin da ake hira dashi a gidan talabijin din Arise wanda The PUNCH suka dauka.

Sanwo-Olu yace shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin da shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, sun kira shi a waya ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel