EndSARS: Akwai yuwuwar mu sassauta dokar kulle a ranar Juma'a - Sanwo-Olu
- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da lokacin da zai cire kulle a wata hira da aka yi da shi
- A cewarsa, matsawar babu kowa a tituna, zai saki kullen da yasa a ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba
- Ya ce da zarar al'amura sun daidaita, babu makawar sakin kullen, don a cigaba da komai kamar da
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, ya bayyana ranar da zai cire kullen da yasa a jihar Legas.
A wata hira da gidan talabijin din Arise suka yi da gwamnan, ya ce za'a cigaba da shige da fice a jihar daga ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba.
Sanwo-Olu yace zai aiwatar da hakan matsawar rikicin ya yi kasa.
A cewarsa, "Matsawar masu zanga-zangar EndSARS suka bar tituna, zuwa gobe zan saki kullen, yadda al'amura zasu koma yadda suke."
KU KARANTA: Dole a sallami shugabannin tsaro, ka sauya salon mulki - Dattawan arewa

Asali: Twitter
KU KARANTA: Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi
A wani labari na daban, fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga gwamnonin da suka sa kulle a jihohin su saboda rikicin SARS da su yi gaggawar dakatar da sojojin da gwamnatin tarayya ta tura jihohin.
Ya rubuta wannan sakon ne a ranar Laraba a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayi magana cikin matsananciyar damuwa, inda yace sojojin dake Lekki toll gate a Legas suna kashe masu zanga-zanga a ranar Talata da daddare bayan saka kullen awanni 24 da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu yayi.
Marubucin yace, "Ga gwamnonin da ya shafa, akwai abinda yafi dacewa kuyi: Ina bukatar ku cire wadannan sojojin. Kuyi gaggawar hada taro don yin gyara aka al'amarinnan."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng