EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

- DSS ta musanta zargin da ake yi wa jami'ansu da taimakon 'yan ta'adda wurin kai wa masu zanga-zangar EndSARS farmaki

- Sun musanta hakan ne a wata takarda da kakakin rundunar, Dr. Peter Afunanya ya gabatar a Abuja

- Ya ce jami'ansu sun yi fice wurin kamala da natsuwa, kuma za su cigaba da hakan, don hakan wannan labarin kanzon kurege ne

Jami'an DSS ba za su taba taimakon masu kai wa 'yan zanga-zangar EndSARS farmaki ba, cewar 'yan sandan farin kaya a ranar Talata.

Jami'an sun killace kawunansu daga masu zanga-zangar kamar yadda suka shaida a wata takarda wadda kakakinsu, Dr Peter Afunanya ya gabatar a Abuja.

Yace babu wani jami'in DSS da aka ga ya kai wa masu zanga-zangar hari.

Kamar yadda takardar tazo: "An janyo hankalin DSS a kan labaran karya da ke yawo akan jami'anmu na taimakon 'yan ta'adda wurin kai wa masu zanga-zangar EndSARS hari a Abuja. Wannan labarin ba gaskiya bane, kuma muna so a yi barin kasa-kasa da makamantan labarin nan.

"Dangane da wannan labarin, mun musanta shi, babu wani jami'in mu da ya aikata hakan. Ba duka mutanen da aka gani cikin kayan kamala bane jami'an mu. Munaso mu tabbatar muku cewa, babu wani jami'inmu da zai yi makamancin hakan.

"Aikinmu na mutanen kirki ne, kuma za mu cigaba da rike martabarmu. Don haka, ku dauki duk wasu labarai makamantan hakan a matsayin na kanzon kurege."

DSS ta yi amfani da wannan damar wurin rokon 'yan Najeriya da su tabbatar sun bi doka kuma sun bayar da hadin kai ga jami'an tsaro.

KU KARANTA: Da duminsa: NECO ta dakatar da jarabawa, ta umarci ma'aikata su koma gida

EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske
EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato ya yi taro da shugabannin gargajiya a gidan gwamnatin Filato don kawo karshen tarzomar da ta barke a jihar, Pemium Times ta wallafa hakan.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya cewa shugabannin gargajiya, su zai kama da laifi matsawar ba'a samu kwanciyar hankali ba a jiharsa sakamakon zanga-zangar rushe SARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel