EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa

EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi kira ga duk wani mai fadi aji a kasar nan da yayi kokarin saka baki a kan zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici

- Lawan ya yi wannan jawabin ne bayan wani taro da suka yi a majalisa da Sifeta janar na 'yan sanda, Adamu Mohammed da Darekta janar na jami'an tsaro na farin kaya, Yusuf Magaji Bichi

- Yace kada shugabanni su yi la'akari da banbancin ra'ayi a siyasa, addini ko kuma yare, su yi kokarin dakatar da matasa daga zanga-zangar da ta canja salo ta koma rikici

Majalisar dattawa ta yi kira ga duk wasu masu fadi aji a kasar nan da su yi kokarin saka baki akan wannan zanga-zangar ta EndSARS da ke ta kara ruruwa a kasar nan.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi wannan kiran ne bayan sun samu labari a kan irin tabarbarewar tsaro da ke kara yawa sakamakon zanga-zangar.

Taron da Sifeta janar na 'yan sanda, Adamu Mohammed, da Darekta janar na jami'an tsaro na farin kaya, Yusuf Magaji Bichi suka samu halarta, Daily Trust ta ruwaito.

A hirar Lawan da manema labarai bayan taron, ya roki duk wasu shugabanni na siyasa da na addini su mike tsaye don dakatar da masu zanga-zangar don samun wanzuwar zaman lafiya.

A cewarsa, "Duk wasu shugabanni, kada su duba banbancin ra'ayi a siyasa, addini ko kuma yare, su tsaya tsayin-daka don ganin an kwantar da tarzomar nan, don gaba daya zanga-zangar ta canja salo".

"Ga dukkan alamu, masu yawo suna rikitar da kasa, basu da wata alaka da zanga-zangar EndSARS.

"Ina amfani da wannan damar ne don in roki duk wasu 'yan Najeriya masu fadi a ji, da su yi kokarin jawo hankalin matasa a kan wannan zanga-zangar don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali," yace.

KU KARANTA: Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule

EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa
EndSARS: Shugabannin DSS da na 'yan sanda sun gana da majalisar dattawa. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni

A wani labari na daban, kungiyar dattawan Arewa tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yayi gaggawar canja salon mulki da yanayin gudanar da aikin sojoji da 'yan sandan Najeriya.

Yayin da Kungiyar ke kira ga matasa da suyi gaggawar kawo karshen zanga-zangar, sunyi kira ga shugaban kasa Buhari, da yayi maza ya sanar da matasa cewa, yaji muryarsu, kuma zai kawo karshen duk wata matsala da ke addabar su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel