Dole a sallami shugabannin tsaro, ka sauya salon mulki - Dattawan arewa

Dole a sallami shugabannin tsaro, ka sauya salon mulki - Dattawan arewa

- Hankalin Dattawan Arewa yayi matukar tashi, inda bayan kira ga matasa da su yi gaggawar ajiye makamansu, sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yadda zai cimma gaci akan rikicin EndSARS

- A wata takarda da dattawa 36 na arewa suka rubuta, wadanda suka hada da Engr Bello Suleiman, Dr Hakeem Baba-Ahmed da Yomi Awoniyi, sun ce wajibi ne canja salon mulki da aiwatar da ayyukan sojoji

- Kungiyar ta kara da cewa, wajibi ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa matasa cewa ya fahimci kukansu kuma zai share hawayensu, yayi kokarin dakatar da kashe-kashen da sojoji keyi don kawo maslaha

Kungiyar dattawan Arewa tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yayi gaggawar canja salon mulki da yanayin gudanar da aikin sojoji da 'yan sandan Najeriya.

Yayin da Kungiyar ke kira ga matasa da suyi gaggawar kawo karshen zanga-zangar, sunyi kira ga shugaban kasa Buhari, da yayi maza ya sanar da matasa cewa, yaji muryarsu, kuma zai kawo karshen duk wata matsala da ke addabar su.

A wata takarda da tazo daga kungiyar dattawan Arewa guda 36, wadanda suka hada da Injiniya Bello Suleiman, Alhaji Mohammed Bello Kirfi, Yomi Awonyi da Dr. Hakeem Baba-Ahmed ta ce: "Jikinmu yayi sanyi a kan yadda baka zaburowa wurin fuskantar baraka a mulkin ka.

"Mun lura cewa, mulkinka baya hobbasa wurin ganin ya kawo karshen duk wata baraka da ta kunno kai, hasalima sai tafiyar tsutsa ake yi wurin kawo karshen wannan zanga-zangar."

Kungiyar ta kara nuna matsalar da za ta iya aukuwa idan har zanga-zangar nan ta cigaba, za ta iya kawo tabarbarewar arzikin kasa, da saka bakin kasashen ketare wanda hakan zai kara lalata kasar.

Sun roki gwamnati da tayi kokarin kawo karshen Boko Haram, ta'addanci da kuma garkuwa da mutane a arewa, su kuma yi gaggawar cigaba da taimakon 'yan gudun hijiran jihohin arewa da kuma kara tsaro a anguwanni.

Ta kara kira ga gwamnati tayi gaggawar daidaitawa da ASUU da kuma komawar jami'o'in kasar nan ta kuma yi kokarin dakatar da kashe-kashe ba tare da kotu ta zartar da hukunci ba.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba sun balle babban kotu a Legas, sun kwashe takardun shari'a

Dole a sallami shugabannin tsaro, ka sauya salon mulki - Dattawan arewa
Dole a sallami shugabannin tsaro, ka sauya salon mulki - Dattawan arewa. Hoto daga @Dailytrust
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni

A wani labari na daban, fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga gwamnonin da suka sa kulle a jihohin su saboda rikicin SARS da su yi gaggawar dakatar da sojojin da gwamnatin tarayya ta tura jihohin.

Ya rubuta wannan sakon ne a ranar Laraba a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayi magana cikin matsananciyar damuwa, inda yace sojojin dake Lekki toll gate a Legas suna kashe masu zanga-zanga a ranar Talata da daddare bayan saka kullen awanni 24 da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu yayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel