Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo

Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo

- Sojoji sun karbe iko da gidan gwamnatin jihar Imo

- Dakarun rundunar soji sun mamaye hanyoyin shiga gidan gwamnatin jihar Imo, 'Douglas House'.

- Sojojin sun yi hakane domin hana fusatattun ma su zanga-zanga samun damar shiga gidan

Da sanyin safiyar ranar Laraba ne sojoji suka isa 'Douglas House' bayan dokar ta bacin da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya saka ta fara aiki, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Dandazon masu zanga-zanga sun yi tururuwar fitowa domin cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da sanarwa da gwamna Uzodinma ya fitar da yammacin ranar Talata.

KU KARANTA: Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamna Uzodinma ya fitar da sanarwar a kurarren lokaci.

Yawanci mazauna jihar, da suka hada da daliban da ke zuwa makaranta, basu san an saka dokar ta baci ta 24 ba.

Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo
Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki

Duk da babu labarin samun wata barna yayin zanga-zangar ENDSARS a jihar Imo, wasu matasa sun yi yunkurin kona wani ofishin 'yan sanda a Ihiagwa.

Da yawan mazauna jihar sun gaggauta komawa gidajensu da yammacin ranar Talata bayan sanar da baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a fadin Najeriya.

A wani labari na daban, Bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta. Gidan yana kan titin Omididun inda suka dinga jifansu da duwatsu.

Gwamna Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci ta sa'o'i 24 a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS a ranar Talata.

Daga bisani sojoji sun shiga lamarin, abinda ya kawo mutuwar a kalla mutane 7 wadanda da yawansu matasa ne.

Bayan wani lokaci, matasan sun yi nasarar kone gidan kurmus.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel