EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma

EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma

- Indai har tarzoma da tashin hankali suka cigaba da aukuwa, to gwamnati za ta kamaku da laifi, cewar gwamna Simon Lalong ga shugabannin gargajiyan jiharsa

- Bayan kullen da gwamnatin jihar Plateau ta sa na awanni 24, matasa sun barke da kashe-kashe, kone-kone da tada tarzoma iri-iri a jihar, har abin ya fara komawa rikicin addini

- Gwamnan jihar ya kirkiri taron gaggawa da shugabannin gargajiya da ke fadin jihar, inda ya nuna musu cewa matsawar rikicin addini ya barke a jihar, to zai shafi arewa gaba daya

Gwamnan jihar Filato ya yi taro da shugabannin gargajiya a gidan gwamnatin Filato don kawo karshen tarzomar da ta barke a jihar, Pemium Times ta wallafa hakan.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya cewa shugabannin gargajiya, su zai kama da laifi matsawar ba'a samu kwanciyar hankali ba a jiharsa sakamakon zanga-zangar rushe SARS.

NAN ta ruwaito yadda Lalong ya saka kulle a kananan hukumomin arewa da kudancin Jos a ranar Talata.

Bayan faruwar hakan ne al'amarin ya kazanta, inda matasa suka yi ta asarar rayuka.

Lalong yace, "Ina umartar ku da ku yi gaggawar daukar matakan da suka dace don kawo karshen tarzomar nan da ta barke a yankunan ku.

"Gwamnati za ta kama ku da laifi matsawar baku dauki matakin da ya dace ba.

"Kuyi kokarin tara matasa ku nuna musu fushinku akan al'amuran da ke faruwa don samun maslaha."

Lalong ya kara da fahimtar da shugabannin cewa, duk wani fadan addinin da ya barke a jihar Jos to tabbas zai iya shafar arewa gabadaya, don haka ya kamata su kawo karshen tashin hankalin tun da wuri.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun damke matashi mai shekaru 30 bayan ya yi wa matar aure fyade a Kano

EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma
EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya

A wani labari na daban, Wasu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne sun balle babbar kotun Igbosere ta jihar Legas, inda suka yi awon gaba da wasu takardun kotun.

A Bidiyon da The Cable suka wallafa, an ga wadanda ake zargin 'yan ta'addan ne suna fita daga kotun da wasu kayan amfanin kotun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel