EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni

EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni

- Fitaccen marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka ya shawarci gwamnatin tarayya a kan kullen da aka saka a jihar Legas

- Ya ce ya kamata gwamnati ta san cewa, ta kashe maciji ne bata sare kansa ba, don yanzu sojojin da suka turo sun maye gurbin jami'an SARS

- Ya ce saka kulle a jihohin da al'amarin zanga-zangar SARS ta shafa ba zai haifi da mai ido ba, don haka yakamata a duba lamarin

Fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga gwamnonin da suka sa kulle a jihohin su saboda rikicin SARS da su yi gaggawar dakatar da sojojin da gwamnatin tarayya ta tura jihohin.

Ya rubuta wannan sakon ne a ranar Laraba a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayi magana cikin matsananciyar damuwa, inda yace sojojin dake Lekki toll gate a Legas suna kashe masu zanga-zanga a ranar Talata da daddare bayan saka kullen awanni 24 da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu yayi.

Marubucin yace, "Ga gwamnonin da ya shafa, akwai abinda yafi dacewa kuyi: Ina bukatar ku cire wadannan sojojin. Kuyi gaggawar hada taro don yin gyara aka al'amarinnan, The Punch ta wallafa.

"Amma kullen awanni 24 ba zai haifi da mai ido ba. Ku yi kokarin shawo kan matasa ta hanyar manyansu a kowacce anguwa, kuma gwamnati tayi kokarin biyan asarorin da aka yi."

Ya kara da cewa, "Abin da ban tausayi da kuma ban takaici, sakamakon cigaba da ruguza kasa da ake yi. Rayuwar mutane ta zama tamkar ta kiyashi, ya kamata gwamnati ta yunkuro.

"Ya kamata gwamnatin tarayya ta san cewa, sojojin da ta turo sun maye gurbin jami'an SARS a wurin kashe-kashen mutane."

KU KARANTA: EndSARS: Dan Najeriya ya maka Twitter a kotu, ya bukaci diyyar $1bn

EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni
EndSARS: Ku gaggauta janye dakarun sojin ku - Soyinka ga Gwamnoni. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kisan fitaccen likitan Kano

A wani labari na daban, Gwamnatin Amurka tace za ta rufe ofishin jakadancinta dake Legas na kwanaki 2 sakamakon zanga-zangar da aketa yi a jihar.

Ta kuma shawarci 'yan kasar da su tabbatar sun kiyayi wuraren da ake zanga-zangar don gudun matsala.

Duk da dai ofishin jakadancin Najeriya basu nuna wanda suke goyon baya ba akan al'amarin zanga-zangar ta shafinsu na Twitter ba. Sun dai sanar da rufe ofishin nasu dake Legas na tsawon kwanaki 2.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel