Da duminsa: Channels TV ta koma aiki bayan sa'o'in da tayi a rufe

Da duminsa: Channels TV ta koma aiki bayan sa'o'in da tayi a rufe

- Sa'o'i kadan bayan daukewar gidan talabijin din Channels, sun dawo aiki kamar da, inda suka cigaba da nuna shirye-shiryensu

- Bayan labarai sun yi ta yawo a kan 'yan ta'addan da suke kokarin kai wa gidan talabijin din hari, ma'aikatan duk sun tsere, inda aka ga gidan talabijin din ya dauke

- A daidai karfe 2:10 ne aka ga gidan talabijin din ya dawo, inda suka cigaba da nuna shirye-shiryen su kamar kullum

Bayan yunkurin kai wa gidan talabijin din Channels da sa'o'i biyu, sun cigaba da aikinsu.

A ranar Laraba da safe ne aka ga gidan talabijin din ya dauke, bayan rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda na hanyar kawo wa gidan talabijin din TVC farmaki.

'Yan jarida da ma'aikatan gidan talabijin din sun tsere saboda tsoron a kawo musu hari, The Cable ta wallafa.

Bayan awanni kadan ne aka ga gidan talabijin din ya dawo an cigaba da shirye-shiryen kamar da, a daidai karfe 2:10 na rana.

KU KARANTA: Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan

Da duminsa: Channels TV ta koma aiki bayan sa'o'in da tayi a rufe
Da duminsa: Channels TV ta koma aiki bayan sa'o'in da tayi a rufe. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, yace hankalin gwamnatin tarayya na wurin matasan Najeriya.

A wata hira da manema labarai suka yi dashi a ranar Alhamis a Abuja, Osinbajo yace, gwamnatin Buhari ta mayar da hankalinta akan duk wani abu da zai taimaki matasa su samu ayyukan yi da bunkasa sana'o'insu.

Don haka ne yace, yakamata matasa su yi amanna da gwamnati, su san cewa a shirye take da ta tallafa musu a koyaushe.

A cewarsa, abinda matasa ya kamata su sani shine, gwamnatin tarayya ta mayar da dukkan hankalinta akansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel