Jami'an tsaro sun damke matashi mai shekaru 30 bayan ya yi wa matar aure fyade a Kano

Jami'an tsaro sun damke matashi mai shekaru 30 bayan ya yi wa matar aure fyade a Kano

- 'Yan sandan jihar Kano sun kama wani Sale Yusuf, wanda ya ke a karamar hukumar tudun wada sakamakon yi wa matar aure fyade

- Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da mai laifin ya amsa laifinsa kuma za'a kai shi kotu

- Mutumin ya yi amfani da wuka wurin tsoratar da matar kafin yayi mata fyade cikin karfi a cikin kauyen Falgore dake karamar hukumar Sumaila

'Yan sandan jihar Kano sun damke wani Sale Yusuf, mazaunin yankin Ana-dariya dake karamar hukumar Tudun-wada dake jihar sakamakon yi wa matar aure fyade a hanyar kauyen Falgore.

Wanda ake zargin yayi amfani da wuka wurin tsoratar da matar kafin yayi mata fyaden, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata takarda, ya ce al'amarin ya faru ne mako biyu da suka wuce, a ranar 6 ga watan Oktoban 2020.

A cewarsa, matar na hanyar komawa kauyen Matigwe da ke karamar hukumar Sumaila, lokacin da ya damketa a kauyen Falgore.

Kiyawa ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma za'a kai shi kotu bayan an gama bincike.

KU KARANTA: Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai

Jami'an tsaro sun damke matashi mai shekaru 30 bayan ya yi wa matar aure fyade a Kano
Jami'an tsaro sun damke matashi mai shekaru 30 bayan ya yi wa matar aure fyade a Kano. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7

A wani labari na daban, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace gwamnati bata da halin samarwa matasa marasa ayyukan yi da suke yawo kwararo-kwararo a titi ayyukan gwamnati, Daily Trust ta ruwaito.

Ngige ya roki ma'aikatu masu zaman kansu da su taimaka su samar wa marasa ayyukan yi wuraren da zasu rabe don kawo karshen rashin ayyuka a kasar nan.

A cewar ministan, kamar yadda takardar ta jami'in hulda da jama'a ya gabatar tace a Abuja a ranar Monday, yayin bude taron samar da ayyuka mai taken : "Samar da cigaban ma'aikatu masu zaman kansu".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel