'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kisan fitaccen likitan Kano

'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kisan fitaccen likitan Kano

- Sabon salon kwacen waya ya fara zama ruwan dare a birnin Jihar Kano, inda masu kwacen ke cin karensu babu babbaka

- Kwanakin baya aka samu labarin kisan wani likitan kashi dake aiki a Asibitin Aminu Kano, sakamakon jayayya da ya yi da masu kwacen waya

- 'Yan ta'addan sukan fake da siyar da ruwa a kan titunan birnin, daga nan suke zagaye motoci da ababen hawa da miyagun makamai

Sabon salon kwacen waya ya jefa mazauna birnin Kano cikin fargaba mai tsanani. 'Yan ta'adda sun fara nisa a harkar kwace a tituna da layukan anguwannin Kano, Daily Trust ta wallafa.

Akwai mutane da dama da suke ji wa ciwo, kai har da kisa. Akwai wani Atiku Shuaibu Ringim, likitan kashi ne a asibitin Aminu Kano wanda suka kashe a watan da ya gabata a kan titin Gwarzo da ke karamar hukumar Gwale.

Masu bincike sun gano cewa an kai masa harin wuraren karfe 8 na dare, inda 'yan ta'addan suka yi kokarin kwace wayarsa amma yaki basu hadin kai, daga nan suka kashe shi har lahira.

Wasu mazauna yankin wadanda suka yi hira da 'yan jarida sun ce masu kwacen kan fake da sayar da ruwan sanyi, da zarar sun ga cunkoso sai su far wa mutanen da ke titin suna kwatar wayoyinsu daya bayan daya.

Wuraren da 'yan ta'addan suka fi kai hari sun hada da kan titin Kofar Dan-Agundi, Gadon kaya, titin Katsina, 'Yan kura kusa da titin France da wasu wurare a Sabon Gari.

Wani da lamarin ya faru dashi mai suna Abba Mahmoud Gwammaja, yace, "Sun kai min farmaki da tsakar rana a wurin kofar Dan-Agundi kusa da Rumfa College. A lokacin akwai cunkoson ababen hawa, sai ga wasu yara da basu wuce shekaru 15 zuwa 20 ba, suna tallan ruwa, kawai sun zagaye mu suna kwacen wayoyi.

"Dukkansu da wukake da sauran miyagun makamai. Daya ya zuro hannunsa cikin mota ta yana umarta ta da in basu wayata, dayan kuma yasa min wuka a wuya, ko da na basu wayar sai da ya yanke ni a hannu".

A satin da ya gabata 'yan sanda suka kama wadanda ake zargi da ta'addanci 67, ana zargin 6 daga cikinsu ne suka kashe likitan nan na Asibitin Aminu Kano. An kamasu da Keke-Napep 4, babura 12 da kuma wayoyi 68.

KU KARANTA: Bidiyon matashi mai digiri na biyu da shaidun makaranta 30 yana tallar kwai

Yadda fashin waya ya zama ruwan dare a Kano
Yadda fashin waya ya zama ruwan dare a Kano. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan

A wani labari na daban, wata mata 'yar Uganda ta shiga cikin mummunan tashin hankali bayan sanin cewa saurayin da take da cikinsa ya aura wata.

Wata mata mai da daya ta sanar da Mywedding.co.ug cewa sun fara soyayya da wani mutum mai suna Norman a 2008, ranar da suka fara haduwa sai soyayyar juna ta ratsa zuciyoyinsu.

Matar tace a ranta tayi yakinin cewa soyayyar su wata rana zata kai ga aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel