Jihar Borno: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP

Jihar Borno: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP

- Dakarun sojin saman Najeriya na cigaba sa samun manyan nasarori a yaki da ta'addanci

- A ranar 19 ga watan Oktoba, dakarun sun ragargaza mayakan ISWAP, maboyarsu da ma'adanar makamansu

- Hakan ta faru ne a karkashin samamen da rundunar Operation Wutar Tabki ta kai yankin tafkin Chadi a Borno

A kokarin dakarun sojin saman Najeriya na jaddada zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso gabas na kasar nan, rundunar Operation Wutar Tabki na cigaba da samun nasarori.

Samamen kwanan nan da dakarun sojin suka kai ya matukar girgiza mayakan ISWAP, sansaninsu da wuraren adana makamai da ke Tumbun Barorowa a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno.

A samamen da dakarun suka kai a ranar 19 ga watan Oktoban 2020 bayan bayanan sirrin da suka samu, sun gano wasu maboyar 'yab ta'addan da suke horar da mayaka.

KARANTA WANNAN: NBA ta sha alwashin maka rundunar soji kotu kan kashe kashen Lekki

Jihar Borno: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP
Jihar Borno: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP - Amnesty International
Asali: UGC

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche ya sanar, ya ce ta jiragen yaki ne aka gano gidajen 'yan ta'addan wadanda suka boye sakamakon bishiyoyin yankin.

A wurin mayakan ta'addancin ke adana makamai bayan sun siyesu daga masu samar musu.

Jiragen yakin sun yi nasarar ragargazasu ta hanyar daukar musu bama-bamai da ya kone yankin.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas

Da yawa daga cikin mayakan ISWAP wadanda aka hango suna kokarin martani ga jiragen sama na yankin duk sun mutu.

Ga bidiyon:

A wani labarin, A ci gaba da dakile laifukan da suka shafi karya tattalin arziki da sauran laifuka makamantan su a shiyyar Kudu maso Kudu, dakarun atisayen SILENT HEAT III ta samu babbar nasara.

A ranar Asabar, dakarun da ke sansanin soji na IBAKA a jiragen su na ruwa sun cafke wani babban jirgi dauke da buhunan shinkafa a hanyar Utan Iyata da aka yi safarar ta daga Kamaru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel