Da duminsa: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya

Da duminsa: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya

- Gwamnatin Amurka za ta rufe ofishin jakadancin ta dake jihar Legas

- Hakan ya biyo bayan zanga-zanga da kuma kullen da aka sa a jihar

- Ta kuma shawarci 'yan kasar da su kiyayi zuwa wuraren da ake zanga-zangar

Gwamnatin Amurka tace za ta rufe ofishin jakadancinta dake Legas na kwanaki 2 sakamakon zanga-zangar da aketa yi a jihar.

Ta kuma shawarci 'yan kasar da su tabbatar sun kiyayi wuraren da ake zanga-zangar don gudun matsala.

Duk da dai ofishin jakadancin Najeriya basu nuna wanda suke goyon baya ba akan al'amarin zanga-zangar ta shafinsu na Twitter ba. Sun dai sanar da rufe ofishin nasu dake Legas na tsawon kwanaki 2.

Kamar yadda suka wallafa: "Duk da Zanga-zangar lumana ake yi, wasu sun fara rikitar da al'amarin. Yanzu haka suna harin ofisoshin 'yan sanda."

"Gwamnatin jihar Legas ta rufe makarantu zuwa wani lokaci, kuma tasa kulle na awanni 24 tun daga karfe 4 na yamma na ranar 20 ga watan Oktoba. Don haka babu kaiwa da komowa a jihar.

"Zamu cigaba da rokon duk wasu 'yan Amurka da su kiyayi duk wuraren da ake zanga-zangar, kuma su cigaba da duba yanar gizo don sanin abubuwan dake faruwa."

KU KARANTA: Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7

Da duminsa: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya
Da duminsa: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya. Hoto daga Vanguarngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala taron sirri da minsitan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin a fadarsa, The Nation ta wallafa.

Duk da har yanzu babu bayani a kan abinda suka tattauna yayin taron, a lokacin rubuta wannan rahoton an gano cewa sun tattauna ne a kan yadda za a shawo kan tarzomar EndSARS da ke ta'azzara.

Idan za mu tuna, a cikin kwanaki biyu da suka gabata an ga yadda zanga-zangar lumanar ta koma zubda jini a sassa daban-daban na kasar nan inda jama'a da kadarori suka salwanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel