EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

- Duk da ba a san abinda suka tattauna ba a ganawar, ana zaton tarzomar da ke karuwa a fadin kasar nan ce

- Duk da kokarin gwamnati na ganin ta cimma bukatun masu tarzomar, a koda yaushe rikicin na cigaba da karuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala taron sirri da minsitan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin a fadarsa, The Nation ta wallafa.

Duk da har yanzu babu bayani a kan abinda suka tattauna yayin taron, a lokacin rubuta wannan rahoton an gano cewa sun tattauna ne a kan yadda za a shawo kan tarzomar EndSARS da ke ta'azzara.

Idan za mu tuna, a cikin kwanaki biyu da suka gabata an ga yadda zanga-zangar lumanar ta koma zubda jini a sassa daban-daban na kasar nan inda jama'a da kadarori suka salwanta.

Duk da gwamnatoci a kowanne mataki sun tashi tsaye wurin tabbatar da bukatu biyar da masu zanga-zangar suka mika, lamarin ya ki ci balle cinyewa kuma hakan yana kawo sabbin bukatu a kowacce rana.

KU KARANTA: Ga lokacin da ASUU za ta janye yajin aiki - Kungiyar da FG sun cimma matsaya

EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugabannin tsaro
EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugabannin tsaro. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace matasa su na da hakkin yin zanga-zanga don sanar da shugabanninsu matsalarsu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce yakamata a ba wa matasa damar bayyanar da damuwarsu da hakkinsu ga gwamnati, amma kada su bar 'yan ta'adda da bata-gari su shiga harkar.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya sanar da hakan bayan taron da yayi da shugaban kasa a fadarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel